Babban Malamin Musulunci Ya Ja Kunnen Ministar Tinubu Kan Hana Aurar da Mata a Niger

Babban Malamin Musulunci Ya Ja Kunnen Ministar Tinubu Kan Hana Aurar da Mata a Niger

  • Yayin da ake ta ceci kan aurar da mata marayu a jihar Niger, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi martani kan lamarin
  • Rijiyar Lemo ya gargadi Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye da ta fita a wannan lamari da bai shafe ta ba
  • Shehin malamin ya bukaci shugabanni musamman Musulmai da su takawa irin wadannan birki saboda gudun matsala

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi martani kan cece-kucen da ake yi game aurar da marayu mata a Niger.

Shehin malamin ya caccaki Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye kan matakin da ta dauka game da shirin aurar da matan.

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

Malamin Musulunci ya magantu kan Ministar Tinubu game da auren mata marayu
Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya bukaci Ministar harkokin mata ta fita sha'anin auren mata marayu a Niger. Hoto: Uju Kennedy-Ohanenye, Dr. Muhd Sani Umar R/Lemo.
Asali: Facebook

Rijiyar Lemo ya gargadi Ministar Tinubu

Rijiyar Lemo ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ce wannan ba hurumin ta ba ne kuma bata daga cikin Musulmai ko kabilar Hausawa da za ta san al'adunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Rijiyar Lemo ya ce a lokacin da aka hallaka iyayensu da sauran mutane a Arewacin Najeriya ba ta yi musu jaje ko tallafa musu da kayan abinci ba.

Ya bukaci shugabannin musamman Musulmai a wannan gwamnati da su takawa mata birki saboda ba za su amince da akida da suka sabawa addini da al'adu ba.

"Wannan Minista ba Musulmai ba ce kuma ba jinsin Hausa/Fulani ba ce ko ƴar Arewa ba wanda ba ta san al'adunmu da addininmu ba, wannan ba aikin da aka dauke ta ta yi ba ne."
"Lokacin da ake hallaka iyayen yara a Zamfara da Katsina da Kaduna da ita kanta Niger ba ta tallafa musu da abinci ko kudi ba, kuma ba ta yi musu jaje ba."

Kara karanta wannan

Niger: Ministar Tinubu ta yi amai ta lashe, ta dauki mataki kan aurar da mata 100

"Amma yanzu tana cewa kada a kuskura a taimaka wurin auren ƴaƴansu, wannan ta shiga hurumin da bai shafe ta ba, saboda bata san al'adunmu da addininmu ba."

- Sheikh Sani Rijiyar Lemo

Minista ta dauki mataki kan auren mata

Martanin malamin na zuwa ne bayan Kennedy-Ohanenye ta shigar da korafi kan kakakin Majalisar jihar Niger.

Uju ta yi korafin ne bayan kakakin Majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji ya shirya daukar nauyin aurar da mata marayu 100 a karamar hukumar Mariga.

Korafin da Ministar ta shigar ya sanya Sarkin-Daji janye kudurinsa na taimakawa wurin aurar da matan a Niger.

Limamai a Niger sun kalubalanci Ministar Tinubu

Kun ji cewa kungiyar limaman jihar Niger sun kalubalanci Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye kan matakin da ta dauka game da auren mata marayu.

Kungiyar ta sha alwashin ci gaba da shirye-shiryen gudanar da bikin da aka shirya a karshen wannan wata da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel