Buhari ne Sila: Shugaban SDP ya Magantu kan Matsin Tattalin Arziki

Buhari ne Sila: Shugaban SDP ya Magantu kan Matsin Tattalin Arziki

  • Shugaban jam’iyyar SDP Shehu Gabam ya dora laifin wahalhalun da Najeriya ke ciki a kan tsohuwar gwamnatin APC da ta shude
  • Shehu Gabam ya bayyana tsohuwar gwamnatin da Muhammadu Buhari ya jagoranta a matsayin silar matsalolin da Najeriya ke ciki
  • Amma ya na ganin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai iya kawo karshen matsalolin sannu a hankali idan an bi matakan da su ka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam ya ce gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce mafi tabarbarewa a tarihin Najeriya.

A cewar Shehu Gabam, a gwamnatin baya ne da Muhammadu Buhari ya jagoranta aka lalata tattalin arzikin kasa, kuma aka fada mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

"Yana hawa Najeriya ta durkushe": Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya soki Tinubu

Muhammadu Buhari
An dora laifin wahala a Najeriya kan gwamnatin Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

'Dan siyasar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi ta shirin Politics Today da kafar Channels Televsion.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Tinubu zai iya magance matsalolin ,” Gabam

Shugaban ya ce matsalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta ya samo asali ne daga gazawar gwamnatin Buhari.

Duk da dai ya na ganin gwamnatin Bola Tinubu za ta iya magance matsalolin, amma sai ta bi sannu a hankali, kamar yadda Naira land ta wallafa.

Shehu Gabam ya ce warware matsalar kasar nan ba zai yiwu cikin rana daya ba domin lalacewar da ta yi.

Shugaban jam’iyyar ya kuma bayar da shawarar ka da a bi hanyoyin da za su kara jefa mutane cikin wahala wajen magance halin da ake ciki.

Ya kara da cewa duk da dai matsalar da ake fuskanta yau gado ce, amma hakkin magance ta ya rataya a wuyan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

Jagoran jam'iyyar adawar ya ba magoya bayan shugaba Tinubu kafar uzuri.

Tinubu zai biyawa Najeriya bashi

A baya mun kawo mu ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan makudan bashin da ake bin Najeriya.

Zai biya bashin N3.3tn da ake bin kasar nan a bangaren wutar lantarki, inda ya ce ana ganin hakan zai magance matsalar wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel