Yan ta'adda
Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan halin rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan jihar Borno. Ta bukaci gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro.
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa 'yan Boko Haram 129,000 ne suka tuba kuma ana ba 800 horo na musamman domin sauya musu hali da tunani.
Sojojin Najeriya sun kama dan bindigar da harsashi ya kare masa yana tsaka da fafatawa da sojin Najeriya a jihar Zamfara. An kama shi ne bayan an kashe wasu.
Gwamnatin Gombe ta ce ba za ta amince wasu bata-gari su tayar da hankula a jihar ba, inda ta umarci jami'an tsaro su gaggauta kamo wanda su ka aikata kisan kai.
Madugun 'yan kungiyar ta'addanci ta Biafra, Nnamdi Kanu ya ja da kotun tarayya yayin masa shari'a. Kanu ya nuna tirjiya a gaban alkali, mai shari'a Binta Nyako.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani kwamandan Boko Haram a Borno mai suna Mulwuta ya yi barazana ga mazauna Banki a karamar hukumar Bama a jihar.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro, sun yi raga-raga da 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a farmakin
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da jikkata wasu da dama.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana tarin nasarorin da dakarun sojoji masu yaki da 'yan ta'adda a sassan daban-daban na Najeriya suka samu a cikin mako guda.
Yan ta'adda
Samu kari