Yan ta'adda
Yayin da al'umma da dama suka gaji da hare-haren yan bindiga a wasu yankunan jihar Katsina, an gudanar da zaman sulhu a Faskari da dan bindiga, Ado Aliero.
Wasu da ake zargi 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ne sun sace wani mutum a karamar hukumar Dukku sun kashe shi bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 5.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa 'yan bindiga sun bukaci a samar musu da asibitoci, makarantu da kafa wajen shan ruwan dabbobi kan sulhu a jihar.
Wasu 'yan ta'adda sun hallaka mutane 22 a wurin da ake ibada a yammacin Nijar, lamarin da ya sake tayar da fargaba a yankin Tillaberi da 'yan jihadi ke addaba.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa an rage matsalar 'yan ta'adda, yan bindiga masu garkuwa da mutane da kashi 70 saboda matakan da Radda ya dauka.
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya musanta rahoton sace masallata 40 inda ya tabbatar da cewa mutane takwas kawai aka dauke a jihar.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zargi tsohon ministan shari'a Abubakar Malami da ingiza ayyukan ta'addanci, abin da ya sa 'yan kasuwa suka guje wa jihar.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa gungun yan bindiga karkashin Ado Aliero aun kashe Hakimin Dogon Dawa a garin Keta, Tsafe a jihar Zamfara.
Dan bindigan da ake nema ido rufe, Ado Aliero ya bukaci a yafi juna duk da kashe rayuka da aka yi a taron zaman lafiya da aka yi a yankin Faskari a jihar Katsina
Yan ta'adda
Samu kari