Yan ta'adda
Rahotannin da muke samu sun ce matashin dan sa-kai ya bude wuta a masallaci a ƙaramar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi inda aka samu raunuka game da lamarin.
Rahotanni sun ce an gudanar da sulhu yau Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025 a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar Katsina domin kare farmakin ’yan bindiga
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan 'yan ta'adda a jihar Kogi. An kashe Kachalla Babangida bayan an bude wa 'yan bindiga wuta a wani dagi da suka buya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Rundunar sojoji ta kama wata mata mai suna Fatima Isah Ile a Kanoma, bisa zargin taimakawa ‘yan ta’adda wajen ayyukansu.
Rundunar ’yan sanda a jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkata 15 a yayin harin yan bindiga da aka kai wajen masu zaman makoki.
Rahotannin sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari kan masallata a garin Matazu da ke Katsina, inda aka kashe wasu tare da jikkata wasu daga ciki.
Bayan cafke wasu daga cikin kwamandojin kungiyar Ansaru, Kotu da ke zamanta a birnin Abuja ta yanke hukunci kan Mahmud Usman, kwamandan Ansaru, hukuncin shekaru 15.
Sanatan Borno ta Kudu, Mohammaed Ali Ndume ya caccaki masu rokon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori hafsoshin tsaro duba da halin da ake ciki.
Binciken kwa-kwaf da aka gudanar ya karyata bidiyon da ake yadawa, inda ake ikirarin sojojin Najeriya na bai wa ’yan bindiga goyon baya a wani daji.
Yan ta'adda
Samu kari