Boko Haram Na Kara Kamari a Borno, an Kashe Mutane a Sabon Hari
- An bayyana samun sabon harin ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno, inda mutane da dama suka rasa rayukansu
- Rahoto ya kuma bayyana matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin tabbatar da an dakile aukuwar hakan a gaba
- Jihar Borno na daga jihohin da suka fi shan fama da ‘yan ta’addan Boko Haram shekaru sama da 10 da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Borno - Akalla mutane tare ne suka rasa rayukansu yayin da wasu hudu suka jikkata a wani mummunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai garin Malam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a yankin da ke kimanin kilomita 272 daga birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
A sakon ta’aziyya da gwamnatin jihar ta fitar, Gwamna Babagana Umara Zulum ya aika da tawaga zuwa yankin domin jajanta wa iyalan da abin ya shafa.

Asali: Original
Sai dai gwamnan na ƙasar waje bisa wasu muhimman ayyuka na gwamnati kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka tura ta’aziyya
Tawagar ta kunshi kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Sugun Mai Mele, wanda ya jagoranci ziyarar.
A cewarsa:
“Mun zo ne bisa umarnin Mai Girma Gwamna Babagana Zulum domin mika saƙon ta’aziyya ga al’ummar Malam Fatori sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai kwanan nan.”
Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin Borno da sojoji za su ɗauki matakai masu ƙarfi don kare yankin daga ƙarin hare-hare.
Za a dauki matakai nan kusa
Ya bayyana cewa Malam Fatori na da muhimmanci sosai ga gwamnati saboda matsayinta na dabarun tsaro da tattalin arziki, don haka gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya kuma sanar da cewa za a tura motocin tona rami domin zagaye hedikwatar ƙaramar hukumar da shinge, da nufin hana yuwuwar sake kai hari daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
Mai Mele ya gargaɗi mazauna yankin da kada su kuskura su bai wa ‘yan ta’adda mafaka ko taimako. Ya ce wanda aka kama yana haɗa gwiwa da su zai fuskanci hukunci.
Gwamnatin jihar ta bayar da tallafi na musamman ga waɗanda harin ya shafa. Iyalan waɗanda suka mutu sun samu N500,000 kowanne, yayin da waɗanda suka jikkata suka karɓi N250,000 kowanne.
Magana kan ‘yan gudun hijira a Borno
A nasa bangaren, Kwamishinan Watsa Labarai, Usman Tar, ya bayyana cewa gwamnati na shirin maido da gidaje 3,000 na ‘yan gudun hijira zuwa Malam Fatori, wanda hakan zai kai adadin iyalai 5,000 da aka koma da su gida gaba ɗaya.
A cewar Tar:
“Tun da farko gwamnatin Borno ta maido da iyalai 2,000, kuma yanzu muna shirin ƙara 3,000 domin cika 5,000.”
Ya kuma tabbatar da cewa za a samar da duk wasu tsare-tsaren tsaro da kayan more rayuwa domin tabbatar da zaman lafiyar mutanen da aka dawo da su.
Kwamishinan ya roƙi jama’a da su rika kai rahoton duk wani abin da suka ga yana da haɗari ga hukumomin tsaro domin hana kai hari a gaba.
Asali: Legit.ng