Yan ta'adda
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauƙe da makamai sun kai mummunan farmaki a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka halaka mutum ɗaya da sace wasu mutum biyar.
Tsagerun 'yan bindiga sun yi ajalin rayuka biyar yayin da suka kai hari garin Duhuwa a karamar hukumar Wurno a jihar Sokoto. Maharan sun kuma raunata mutum hudu.
Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasarar dakile mummunan harin 'yan 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Gezawa da ke jihar Kano.
Dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƴan sakai sun samu nasarae ceto mutum huɗu da miyagun ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kebbi.
Wasu miyagun ƴan ta'adda sun tare babban titin hanyar Funtua-Gusau inda suka halaka mutane masu yawa tare da yin awon gaba da wasu masu yawa a wani hari.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zaman makokin kisan matasa 17 da Boko Haram ta yi a jihar Yobe, wank ya sake tashi da masu zuwa jana'iza, an rasa rayuka 20.
Mayakan Boko Haram sun yi ajalin wasu matasa 17 a jihar Yobe saboda matasan sun ki bin umarninsu na biyan kudin haraji kamar yadda su ka umarce su.
Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna ida suka salwantar da ran mutum ɗaya. Ƴan bindigan sun kuma sace mutum 25.
Wasu ƴan ta'adda mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun salwantar da rayukan mutim 16 a wani ƙazamin hari da suka kai ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.
Yan ta'adda
Samu kari