Filato: Mazauna Garin Mangu Sun Fadi Wadanda Ke da Hannu a Kashe-Kashen da Ake Yi

Filato: Mazauna Garin Mangu Sun Fadi Wadanda Ke da Hannu a Kashe-Kashen da Ake Yi

  • Mazauna garin Mangu da ke jihar Filato sun zargi jami'an tsaron da jihar ta kafa wajen haddasa kashe-kashe da kona gidaje a garin
  • Wani mazaunin garin mai suna Salisu Mu'azu, ya ce jami'an 'Operation Rainbow' sun farmaki mutane da harbi da kona masu muhalli
  • An gano cewa an kashe gomman mutane da kona gidaje da dama a garin Mangu as ranar Laraba, duk da dokar zama gida da ka saka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Mangu, jihar Filato - Al'ummar da ke zaune a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato sun zargi jami'an tsaron jihar na 'Operation Rainbow' da aikata laifukan kisan kai da kona gidaje.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa

Mazauna garin sun zargi jami'an 'Operation Rainbow' ne kan jagorantar 'yan daba su kashe mutane ko su kona masu gidaje, inda suka ce an ci gaba da kai masu hare-hare a ranar Laraba.

Rikicin Filato: Ana zargi jami'an 'Operation Rainbow' da kashe mutane da kona gidaje a Mangu
Rikicin Filato: Ana zargi jami'an 'Operation Rainbow' da kashe mutane da kona gidaje a Mangu. Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Yadda jami'an Operation Rainbow ke ta'addanci a Kwata

Salisu Mu'azu, wani mazaunin garin Kwata, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa 'yan bindiga bisa jagorancin Operation Rainbow sun shiga kauyen misalin karfe 9:30, inda suka rinƙa harbi da kona gidaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Jami'an Operation Rainbow za su jagoranci 'yan bindigar, za su je wajen mutane da sunan suna ran gadi, amma ba haka ba ne. Muna cikin babbar matsala."

Jami'an Operation Rainbow sun hana binne gawarwaki a Femawa

Ibrahim Isa, mazaunin Anguwan Femawa, ya ce jami'an 'Operation Rainbow' da 'yan daba sun farmaki kauyen su.

Ya ce:

"A yanzu dai ba wata doka a Mangu, duk inda ka je za ka ji harbin bindiga da kashe mutane. Ba mu san adadin mutanen da suka mutu ba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

"A halin yanzu ba mu samu damar binne gawarwakin wadanda muke da su a kasa ba, kuma har yanzu ana ci gaba da kashe mu ba wai daina wa suka yi ba."

Operation Rainbow sun koma kashe mutane a Mangu - Salisu

Musa Salisu, mazaunin Hayi a Mangu, ya bayyana irin aika-aikar da jami'an tsaron Operation Rainbow ke yi a garin su.

Ya ce:

"Muna rokon gwamnatin tarayya ta kawo mana dauki, domin jami'an Operation Rainbow da aka samar da tsaron al'umma yanzu su ke kashe mu da kona mana gidaje.

Sai dai jami'in hulda da jama'a na Operation Rainbow, Panam Gongden, ya ƙaryata masu wannan zargi, inda ya ce babu wani jami'i da ya kashe wani ko kona gidan wani.

Mayakan ISWAP sun kai wa Boko Haram sabon farmaki

A wani labarin kuma, mayakan ISWAP sun kai wani sabon farmaki a sansanin mayakan Boko Haram da ke Tumbun Jaki a ranar 21 ga watan Janairu.

An ruwaito cewa Boko Haram ta rasa mayakanta da dama a wannan harin wanda ISWAP ta kaddamar don ramuwar gayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel