An Kama Ciyaman Din PDP Da Wasu Mutane 2 Kan Safarar Bindigu a Zamfara

An Kama Ciyaman Din PDP Da Wasu Mutane 2 Kan Safarar Bindigu a Zamfara

  • Dakarun Sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun kama wasu mutane uku da ake zargin suna safarar muggan makamai zuwa jihar Zamfara
  • Mutanen da aka kama a kan iyakar Illela da ke jihar Zamfara sun hada da wani da aka ce shugaban jam'iyya ne a gundumar Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Shinkafi
  • Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron sun samu ingantattun bayannan sirri ne dangane da wadanda ake zargin kuma suka kafa shingen bincike suka cafke su a hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Zamfara - Tawagar Hadin Gwiwa na Jami'ar Tsaro (JTF) na Operation Hadarin Daji ta kama wasu mutane uku da ake zargi masu safarar bindigu ne zuwa Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan Bindiga sun yi garkuwa da shugaban hukumar gwamnati a jihar PDP

An kama ciyaman din PDP da wasu kan zargin safarar bindigu a Zamfara
Jami'an tsaro sun kama wasu da ke sayarwa yan bindigan Zamfara makamai ciki har da wani da aka ce ciyaman ne na PDP. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda ake zargin, akwai wani da aka ce shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne a gundumar Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Shinkafi na jihar Zamfara.

Yadda aka kama ciyaman din jam'iyyar a Zamfara

PRNigeria ta tattaro daga majiyar tattara bayanan sirri na sojoji a jihar cewa Ibrahim, da abokan harkarlarsa, Musa Usman Seun da Isah Mohammed, duk an kama su a ranar Litinin.

Majiyar ta kara da cewa:

"Dakarun hadin gwiwa na Operation Hadarin Daji na shiyyar Arewa maso Yamma sun samu ingantattun bayanan sirri game da ayyukan wani hatsabibin mai dillancin bindigu da ke nufin fasakwabrin makamai zuwa Zamfara, nan take sojojin suka kafa shingen hanya kuma suka kama mutum 3 da ake zargi.
"Mutane ukun da ake zargi suna Musa Usman Suen, Aminu Ibrahim, da Isah Mohammed da aka kama a baya-bayan nan a Shinkafi a ranar 22 ga watan Janairun 2024, an kwace tsabar kudi naira miliyan biyu da dari biyar da dubu tamanin, mota kirar Volkswagen Wagon, wayoyin salula 3 da wasu kayan daga hannunsu."

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane 30 sun mutu yayin fada tsakanin sojoji da 'yan bindiga a jihar Arewa, bayanai sun fito

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Binciken farko da aka gudanar sun nuna cewa makuden kudin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin an biya su ne domin wasu makamai a iyakar Illela a jihar Sokoto. Ana cigaba da bincike kan wadanda ake zargin."

Fada Tsakanin ISWAP da Boko Haram Ya Yi Ƙamari Yayin Da Suka Kashe Juna a Sabon Rikici

A wani rahoton kun ji cewa rikici tsakanin mayakan Boko Haram da yan ISWAP a Tafkin Chadi, na cigaba da yin kamari inda aka kashe da dama a bangarorin biyu.

Sabon rikicin wanda ya fara a ranar Asabar ya cigaba har zuwa ranar Lahadi 21 da watan Janairu, ya samo asali ne yayin da tawagar jiragen ruwan Boko Haram takwas dauke da mayaka 15 suka kai wa yan ISWAP hari a Tumbin Jaki, Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel