Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Farmaki ’Yan Gudun Hijira a Jihar Arewa, an Rasa Rayuka

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Farmaki ’Yan Gudun Hijira a Jihar Arewa, an Rasa Rayuka

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu 'yan gudun hijira a Wukari, jihar Taraba a ranar Alhamis, kuma sun kashe mutane da dama
  • Yayin da ake zargin cewa 'yan bindigar mayakan kabilar Jukun ne, an ruwaito cewa sun nemi 'yan gudun hijirar su tashi daga matsugunnin su
  • Shugaban kabilar Tiv a jihar Taraba, Cif James Baka, ya roki Gwamna Kefas wanda dan asalin Wukari ne da ya kawo masu dauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Taraba - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kabilar Jukun ne sun kai hari tare da kashe wasu ‘yan gudun hijira biyu da suka dawo gida a Ikyenum, karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Maza gabanku: Dakarun sojoji sun buɗe wa ƴan bindiga wuta, sun kashe da yawa a jihar arewa

Wukari dai karamar hukumar Gwamna Agbu Kefas ce, sai dai kuma kashe-kashe da ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan gudun hijira a yankin na karuwa a ‘yan kwanakin nan.

'Yan bindiga sun kai hari kan 'yan gudun hijira a Taraba
'Yan bindiga sun kai hari kan 'yan gudun hijira, sun kashe mutane da dama a jihar Arewa. Hoto: APF
Asali: Getty Images

A makon da ya gabata ne ‘yan gudun hijirar suka yi korafi game da barazanar da ‘yan kabilar Jukun da ke yi wa rayuwarsu tare da yin kira ga Gwamna Kefas da ya ba su tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigar sun nemi 'yan gudun hijirar su bar muhallansu

Shugaban kungiyar kabilar Tibi ta jihar Taraba, Cif James Baka, ya shaida wa Tribune Online cewa makasan sun tunkari ‘yan gudun hijirar, inda suka bukaci su bar gidajensu.

Jim kadan da tafiyarsu ne suka yo ayari dauke da makamai suka dawo wajen 'yan gudun hijirar, suka aiwatar da kisan.

A cewar shugaban ‘yan kabilar Tibi na jihar, wasu da suka tsira sun bayyana cewa maharan sun zo da yawa kuma suka fara harbin wanda duk suka hadu da shi.

Kara karanta wannan

PDP vs APC: Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar gwamnan jihar Sokoto

Martanin rundunar 'yan sanda kan harin

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bakin PPRO Usman Abdullahi ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ba wannan ne karon farko da ake tashin hankali tsakanin 'yan kabilar Jukun da Tiv ba, wanda ke kai ga irin wannan farmakin, kamar yadda jaridar Premium Times ta taba ruwaitowa.

An kwantar da Sarki Charles a asibitin Landan

A wani labarin, Sarkin Burtaniya, Charles III tare da sarauniyarsa Camilla, sun isa wani asibitin kudi da ke Landan don duba lafiyar basaraken.

An ruwaito cewa rashin lafiyar sarkin ta tsananta inda ake hasashen za a yi masa aiki a mafitsara don cire wata 'ƙaba' da ta kara yaduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel