‘Falle 1 ce’; Jigon Matasa a APC Ya Bar Jam’iyya, Ya Hango Shan Kashi a 2027
- Sahabi Sufiyan ya raba gari da jam’iyyar APC da ya shafe shekaru a cikinta kuma har ya taba neman kujera a majalisar NWC a 2023
- Ya koka cewa APC-Sokoto ba su son jawo matasa masu tunani, ya ce duk wani matashi da ya san abin da yake yi, ba a damawa da shi
- Matashin bai fadi jam’iyyar da zai koma ba, amma ya zargi gwamnatin APC da gaza magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
M. Malumfashi ya shafe shekaru kimanin 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sokoto - Legit Hausa ta samu labarin cewa Sahabi Sufiyan ya yi sallama da jam’iyyar APC mai mulki, zai shiga cikin ‘yan adawa a yaki gwamnati.
Malam Sahabi Sufiyan ya koka a kan yadda abubuwa suke faruwa a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a Najeriya da Ahmad Aliyu a Sokoto.

Source: Facebook
Sahabi Sufiyan ya rabu da jam'iyyar APC
A wata hira ta musamman da Sahabi Sufiyan a ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu 2026, ya tabbatar wa Legit Hausa cewa ya yi sallama da jam’iyyar APC.
Matashin ya shaida mana cewa zuwa yanzu bai yanke shawarar jam’iyyar da shi da mutanensa za su shiga ba, amma suna tuntubar masoyansu a Illela.
Da muka tambaye shi ko zai shiga jirgin jam’iyyar ADC da ta fara yi wa APC barna a Sokoto, ya ce zai sanar da matakin da za su dauka ba da jima wa ba.
Akwai yiwuwar matashin APC ya fada ADC?
Sahabi Sufiyan ya kuma bayyana mana cewa ba abin mamaki ba ne a gan shi tare da Sanatan Gabashin jihar Sokoto, Ibrahim Lamido cikin ADC.
“Ba za mu ce guguwar APC ce ta ke kwasarmu ba. Amma idan komai yana tafiya daidai a kasa, babu wata guguwa da za ta tafi da ‘yan jam’iyya.
Idan ana aiki, ‘yan jam’iyya musamman wadanda suka yi amfani da dukiyarsu da karfinsu da lokacinsu wajen kawo gwamnati, ba za su sauya sheka ba.”
- Sahabi Sufiyan

Source: Facebook
Sufiyan wanda ya taba neman zama shugaban matasan APC na kasa ya ce siyasar Lamido tana ba shi sha’awa domin yana tafiya da talakawa.
Baya ga haka, ya ce ‘dan majalisar dattawan yana ganin darajar mutane, akasin abin da yake zargin yana faruwa a jam’iyyar APC mai mulki a yau.
A wasikar da ya aiko wa Legit, matashin ya koka da yadda ba a ba matasa dama a APC, sannan ya ce ba a tafiya da wadanda suke da ra’ayin kansu.
2027: 'Falle 1 ce ga APC'
A hirar mu da shi, shugaban gamayyar na kungiyar matasa da matan APC ya ba ‘yan jam’iyyar a Sokoto shawara ‘su tsaya su bude ido, su kara dubawa’
Ya fada mana cewa mutane masu daraja za su tsere domin kusan duk matasan da suka yaki PDP a 2023 a yau suna kuka da mulkin APC a sama da kasa.
Daga cikin abubuwan da ya koka da su ga shugaban APC a mazabarsa shi ne matsin tattalin arziki da gaza kawo karshen rashin tsaro baya ga yakar ‘yan adawa.
Har ila yau, Sufiyan ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kokarin ganin bayan ‘yan adawa, wanda ya ce hamayya ita ce gishirin damukaradiyya a duniya.
Zainab Buba Galadima ta fita daga APC
Ɗiyar Buba Galadima, Zainab Buba Galadima ta zargi APC da yi wa ƴan Najeriya shigo-shigo ba zurfi kamar yadda labari ya gabata a farkon makon nan.
Zainab Buba Galadima ta kwatanta salon mulkin APC a karkashin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu.
'Yar siyasar ta bayyana yadda ta sha wahala a APC bayan shekaru fiye 10 ana dama wa da ita kuma har ta samu mukami a lokacin Farfesa Yemi Osinbajo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


