Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

  • An kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa ba tare da an samu wata babbar matsala ba
  • Jam’iyyar APC ta dauko wadanda za su rike mata majalisar NWC a kasa ta hanyar yin maslaha
  • ‘Yan takarar da ba su dace ba, sun nuna dangana ba tare da sun kowOwa jam’iyya rikicin komai ba

Abuja - A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bi wasu daga cikin wadanda suka saye fam da niyyar takara, amma ba su yi nasarar samun mukamai a APC ba.

Jiya Tanko Al-Makura ya fitar da jawabi na musamman, ya ziyarci Abdullahi Adamu domin yi masa fatan alheri bayan ya doke shi a zama shugaban APC.

Punch ta ce Sanata Tanko Al-Makura ya nuna Ubangiji ne yake bada mulki, don haka ya taya Adamu murna, tare da kira gare shi da ya mara masu baya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Ismail Ahmed Buba wanda ya yi takarar sakataren gudanarwa na kasa, ya karbi sakamakon da ya ji.

“Ina godiya da kowa. Mun yi kokari a daren da ya gabata. Marada ba su yi tunanin za mu kawo nan ba. Sai mu je wani yakin na gaba. Na gode!!” - Ismail B. Ahmed

Abiola ta taya Israel murna

Rinsola Abiola wanda ta nemi kujerar shugabar matasan jam’iyyar APC na kasa tayi amfani da shafinta na Twitter, ta bayyana cewa ta amince da kaddara.

Takara a APC
Taron APC na kasa a Abuja Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Da take magana a Twitter, Abiola ta godewa Allah, ta jinjinawa wadanda suka taya ta yakin zabe.

“Na kira abokina, kuma jagora na a yanzu @dayoisrael a game da zamansa shugaban matasa na jam’iyyarmu ta APC.
Ina sa ran aiki da shi, tare da masa fatan alheri.” - Rinsola Abiola

Kara karanta wannan

Zaben Shugabanni: APC ta bayyana abubuwan da za a zo dasu filin taron gangami

Sauran masu harin jagorancin matasa

Olusegun Dada ya fitar da jawabi na musamman, yana cewa maslahar jam’iyya ta sha gaban burinsa, don haka ya amince da matakin da APC ta dauka.

Sahabi Sufyan ya nemi mukamin mataimakin shugaban matasa na kasa, amma bai dace ba. Duk da haka ya yi godiya ga Ubangiji, ya sallamawa jam’iyyarsa.

A cewar Sufyan, ya kara samun gogewa da sanin jama’a a jam’iyyar APC a takarar da ya yi.

A wani bidiyo kuwa, an ji sai da Adebayor Shittu ya caccaki Bola Tinubu kafin ya janye takararsa. Shittu ya nemi mukamin mataimakin shugaban jam’iyya.

Sabon shiga APC ya zama Sakatare

An ji yadda Sanata Iyiola Omisore wanda ya fito daga jihar Osun ya zama sabon jam’iyyar APC mai mulki na kasa a NWC bayan shekara guda da sauya-sheka.

Har zuwa bayan zaben 2019, Iyiola Omisore yana tare da jam’iyyar adawa, bai shiga APC ba sai farkon 2021. Yanzu shi ne zai dare kan kujerar sakatare na kasa.

Kara karanta wannan

Atiku, Ribadu, Tambuwal, da wadanda suka yafe neman Shugaban kasa, su ka nemi Gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel