2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari

2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari

  • Tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Borno, Kashim Ibrahim-Imam, yayi magana game da zaben 2023
  • Ibrahim-Imam ya ce wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari ba zai fito daga kudu maso kudu da kudu maso gabas ba a 2023
  • A cewarsa, jam’iyya mai mulki na iya zabar dan takararta daga yankin arewa da kudu maso yamma

Maiduguri, Borno - Kashim Ibrahim-Imam, jigo a jam'iyyar ya rufe hasashen fitowar dan takarar shugaban kasa na APC daga shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sau biyu, wanda a yanzu jigo ne na APC, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a wani shiri na Arise TV.

Kara karanta wannan

A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

2023: Fitaccen jigon APC ya bayyana yankin da zai samar da wanda zai gaji Buhari
Fitaccen jigon APC, Kashim Ibrahim-Imam ya bayyana cewa jam'iyyar ba za ta zabi magaji Buhari daga kudu maso kudu da kudu maso gabas ba Hoto: APC
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban hukumar kula da asusun manyan makarantu (TETFUND), Ibrahim-Imam, ya ce jam’iyya mai mulki ba ta da karfi a shiyyar kudu maso kudu da kudu maso gabas, saboda haka ba za ta zabi dan takararta daga shiyyoyi biyun ba.

Wanda zai gaji shugaba Buhari zai iya fitowa daga arewa, kudu maso yamma

Jigon na APC wanda bai tsayar da dan takarar arewa ba ya ci gaba da cewa jam'iyyar mai mulki tana da karfi a dukkan shiyyoyin arewa da kudu maso yamma.

Ya ce bai da masaniya a kan kudirin Honorabul Rotimi Amaechi na tsayawa takarar Shugaban kasa.

Jigon na APC ya lura cewa:

“Ina tunawa a kwanakin da nake a matsayin mai ba shugaban kasa shawara a majalisar tarayya lokacin da sanatocin Action Congress of Nigeria (ACN) da marigayi Wahab Dosumu ke jagoranta suka tsallake daga ACN zuwa PDP. . PDP ba ta je kotu ba a lokacin. Abokina Sanata Musilium Obanikoro ya sauya sheka a lokacin, PDP ba ta je kotu ba."

Kara karanta wannan

Ban nemi kotu ta kori Buni a matsayin Gwamnan Yobe ba - Dan takarar gwamnan PDP

Kashim-Imam wanda ya kare sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, daga PDP zuwa APC, ya yi watsi da karar da babbar jam’iyyar adawa ta shigar domin kalubalantar matakinsa a matsayin aikin ilimi kawai.

Ya kuma yi ikirarin cewa tsohuwar jam’iyya mai mulki ce ta gabatar da sauya shekar gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya daga adawa zuwa jam’iyya mai mulki.

Muna tsakar tattaunawa da Gwamnonin PDP 2 da za mu shigo da su APC inji Jigon Jam’iyya

A gefe guda, Alhaji Kashim Ibrahim-Imam, ya bayyana cewa suna tattauna wa da wasu cikin gwamnonin jam’iyyar adawa.

A ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, jaridar Daily Trust ta rahoto Kashim Ibrahim-Imam yana cewa suna neman jawo wasu gwamnoni biyu da ke PDP.

Kashim Ibrahim-Imam bai kama sunayen wadannan gwamnoni da jam’iyyar APC ta ke zawarci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng