Shirin Kifar da Tinubu: Kwankwaso Ya Tara Obi, Naja'atu, Manyan ADC da PDP a Kano

Shirin Kifar da Tinubu: Kwankwaso Ya Tara Obi, Naja'atu, Manyan ADC da PDP a Kano

  • Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron barka da sallah na 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa manyan 'yan adawa da suka fito daga jam'iyyun ADC da PDP a Najeriya sun halarci taron 'yan Kwankwasiyyar
  • An bayyana cewa hakan wani sako ne da 'yan adawa suka isar da ke nufin hada karfi da karfe wajen kalubalantar Bola Tinubu a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da ake shirin tunkarar siyasar 2027, gwamnonin jam’iyyar PDP; Seyi Makinde da Bala Mohammed sun fara ganawa da 'yan adawa.

Wata tawagar 'yan adawa da ta hada da Peter Obi, gwamna Seyi Makinde, Hajiya Naja'atu Muhammad sun hadu a gidan Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Ana ruguntsumin Sallah, 'yan bindiga sun kai hari, an sace masu ibada

Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi, Najatu Muhammad
Rabiu Kwankwaso, Peter Obi da wasu manyan 'yan siyasa a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X cewa ya gana da 'yan adawar ne a gidansa da ke Miller Road a jihar Kano.

Kwankwaso ya tara 'yan adawa

A ranar Lahadi, gwamna Makinde da shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed, sun yi wata ganawar sirri da Sanata Seriake Dickson, wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma, a Bauchi.

Daga bisani, Makinde da Dickson suka tafi Kano, inda suka hadu da Kwankwaso, tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi.

A hotunan da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, an hango manyan 'yan adawa daga jam'iyyu daban-daban a wajen taron.

Me ya kai 'yan adawa gidan Kwankwaso?

Duk da cewa bayyana taron a hukumance a matsayin na bukukuwan sallah, majiyoyi na kusa da Kwankwaso sun nuna cewa tattaunawar na iya nasaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Ana shagulgulan Sallah, ƴan ta'adda sun sace jami'in gwamnatin jihar Kano

Sa’o’i kadan bayan ganawar Bauchi, Makinde da Dickson sun isa Kano domin halartar taron Dandalin Kwankwasiyya karo na 10 na shekara-shekara.

Kwankwaso da wasu 'yan adawa a Kano
Gwamna Seyi Makinde a hagu, Rabiu Kwankwaso a tsakiya, Sanata Seriake Dickson a dama. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Dandalin Kwankwasiyya muhimmin taro ne ga mabiya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ake samun damar mu’amala, tattaunawa da kuma bukukuwa.

Masu shirya taron sun ce hakan na taimakawa wajen karfafa alaka ta siyasa da kuma hada kan jama’a domin shirye-shiryen gaba.

Wata majiya kusa da Rabiu Kwankwaso ta bayyana cewa, bayan shagalin sallah, ziyarar ta kunshi muhimman tattaunawa na siyasa.

Punch ta wallafa cewa majiyar ta ce:

“Saboda dokokin zabe da kuma wa’adin sauya sheka, ana ci gaba da tattaunawa. Duk da cewa an yi taron ne a lokacin Eid-el-Fitr, yana daga cikin shirye-shiryen zaben 2027.
“Za ka ga akwai wadanda ke da niyyar takara. Akwai shugabannin PDP, akwai jagoran NDC sannan akwai Peter Obi tare da jagoranmu Kwankwaso.
“Don haka, za a tattauna batutuwa da suka shafi 2027, hadakar siyasa da sake tsara sahu. Ina ganin nan da kwanaki masu zuwa, alkiblar da suke nufi za ta bayyana ga ‘yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Azumi ya zo karshe: Daular Larabawa ta sanar da ranar hawan idin karamar Sallah

Nasihar Mansur Sokoto kan 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya yi nasiha game da makomar siyasar Najeriya a zaben 2027 mai zuwa.

Malamin ya yi gargadi da cewa akwai bukatar malaman addini su kaucewa kamfen da salon Muslim Muslim da Bola Tinubu ya kawo.

Ya bukaci a rika bayyana ayyuka da nasarorin shugaban kasar domin jama'a su tantance ko ya kamata ya koma wa'adi na biyu ko a'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng