Bayan Rasa Abba Kabir a Kano, Kwankwaso Ya Ziyarci Gwamnan PDP har Gida

Bayan Rasa Abba Kabir a Kano, Kwankwaso Ya Ziyarci Gwamnan PDP har Gida

  • Yayin da siyasar zaben 2027 ke kara zafi, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wata ziyara ta musamman ga gwamnan PDP a Najeriya
  • Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa Kwankwaso ya gana da Gwamna Seyi Makinde a Ibadan cikin sirri da ta jawo hasashe kan zaben 2027
  • An gudanar da ganawar a gidan gwamnatin Oyo, yayin da ake rade-radin kulla kawancen siyasa gabanin takarar da za a gwabza a badi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso na ci gaba da shirye-shiryen zaben 2027.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Rabiu Musa Kwankwaso na ganawa a sirrance da Gwamna Seyi Makinde a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Kwankwaso ya je gidan gwamnan PDP domin ziyara
Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Seyi Makinde. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Seyi Makinde.
Source: Facebook

Rahoton Tribune ya wallafa bidiyon ziyarar Kwankwaso ga Makinde a ibadan yayin da ake ci gaba da maganganu bayan Gwamna Abba Kabir ya bijire wa jagoran na Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Rokon majalisar jihar Kano ga Abba Kabir game da zargin Amurka kan Kwankwaso

Siyasar 2027: Ganawar Makinde, Atiku da IBB

Lamarin na zuwa ne makonni kadan bayan Makinde da tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun ziyarci gidan tsohon shugaban mulkin soja a Minna, Niger, a wani mataki da ake dangantawa da tuntubar siyasa gabanin zaben 2027.

Kwankwaso ya dawo Najeriya ne ta filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan abin da jam’iyyar NNPP ta bayyana a matsayin “muhimman tattaunawa na kasa da kasa” a India.

Dawowarsa ya biyo bayan rahotannin wani kudirin doka a gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda aka ambaci sunansa cikin mutanen da aka ba da shawarar kakaba musu takunkumi kan zargin take ‘yancin addini a Najeriya.

Kwankwaso ya gana da gwamnan PDP
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso yana ganawa da Gwamna Seyi Makinde

Ana gudanar da ganawar a gidan gwamnatin Oyo da ke Ibadan, babban birnin Oyo, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar

Majiyoyi sun nuna cewa ana alakanta wannan ganawa da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027, wanda tuni ya fara daukar hankalin ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Abba yayin buda baki da gwamnoni

Ganawar ta kara haifar da hasashe kan yiwuwar kulla kawance tsakanin manyan ‘yan siyasa yayin da ake tunkarar babban zaben kasa.

An ce ganawar ta gudana ne ba tare da halartar manema labarai ba, lamarin da ya kara janyo cece-kuce a fagen siyasar Najeriya.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a samu wasu bayanai da ke nunu hakikanin dalilin ganawar ba sai dai hasashe kawai musamman na siyasa.

Me Kwankwaso ya tattauna da Makinde?

Sanatan Rabi'u Kwankwaso ya tabbatar da batun ganawar a shafinsa na Facebook a yammacin yau Laraba 25 ga watan Fabrairun 2026.

Kwankwaso ya ce sun gana ne tare da tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban Najeriya.

Kwankwaso ya sake sukar Abba Kabir

An ji cewa tsohon dan takarar Shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaicin sauya shekar gwamnatin Kano zuwa APC.

Kwankwaso ya ce Allah ne kaɗai ya san dalilin da ya sa gwamnati ta janye jikinta daga da tafiyar Kwankwasiyya, sai dai abin bai yi dadi ba.

Ya jaddada cewa ƙofar Kwankwasiyya a buɗe ga dukkanin wadanda suka bi gwamnati a kowane lokaci idan akwai bukatar haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.