Peter Obi da Jonathan Na Shirin Hadewa don Kifar da Tinubu? An Ji Gaskiyar Zance

Peter Obi da Jonathan Na Shirin Hadewa don Kifar da Tinubu? An Ji Gaskiyar Zance

  • An fara hasashe da jita-jitar cewa Peter Obi da Goodluck Jonathan na shirin hadewa don tunkarar Mai girma Bola Tinubu a zaben 2027
  • Maganganun sun fara yawo ne bayan an ga Peter Obi tare da tsohon shugaban kasan a wasu wurare
  • Sai dai, mai taimakawa Peter Obi kan harkokin yada labarai, Yunusa Tanko, ya fito ya warware zare da abawa kan lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan jita-jitar cewa yana shirin yin hadaka da Goodluck Jonathan a zaben 2027.

Peter Obi ya karyata jita-jitar cewa yana shirin yin haɗin gwiwa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Peter Obi bai shirin hadewa da Goodluck Jonathan
Peter Obi tare da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Dr. Yunusa Tanko, mai taimaka wa Peter Obi kan harkokin yada labarai kuma shugaban kungiyar Obidient Movement Worldwide, a wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar LP ta mika bukata ga Atiku, ta tabo batun janyewar Peter Obi a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace alaka ke tsakanin Peter Obi da Jonathan?

Yunusa Tanko ya ce, duk da cewa Peter Obi da Jonathan suna da kyakkyawar alala, ba su tattauna wani shiri na siyasa ko yarjejeniya game da 2027 ba.

"Mai gidana da tsohon shugaban kasa suna da kyakkyawar fahimtar juna. Don haka ganin suna ganawa ba yana nufin wani abu na siyasa ba. Ganawar ta kasance ne kawai don tattauna yadda za a inganta kasar nan."
“Babu wata yarjejeniya ko tattaunawa kan 2027. Hatta lokacin da suka hadu a Ghana, ni ma ina wurin, kuma babu maganar siyasa a ciki.”

- Yunusa Tanko

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake kira ga jam’iyyun adawa su dunkule waje guda domin fuskantar Shugaba Tinubu da APC a 2027.

Magoya bayan Obi da Jonathan na muhawara

A shafukan sada zumunta, magoya bayan Peter Obi da Jonathan sun shiga muhawara mai zafi, inda wasu ke kira ɗaya daga cikinsu ya janye wa ɗayan don karfafa hadin kan adawa.

Kara karanta wannan

Mutanen da suka ja junnen Jonathan game da sake neman mulkin Najeriya a 2027

Ana hasashen Jonathan da Peter Obi za su yi takara a 2027
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Peter Obi. Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Jonathan, wanda ya jagoranci Najeriya daga 2010 zuwa 2015, yanzu ya koma sahun jagororin da ke shiga tsakani a rikice-rikicen siyasa a Afrika da tallafawa dimokuraɗiyya.

Peter Obi kuwa, wanda ya zo na uku a zaben 2023, ya ci gaba da ganawa da manyan jiga-jigan siyasa a fadin kasar nan, matakin da ake ganin yunkuri neman samun goyon baya ne kan zaben 2027.

An bukaci Atiku ya marawa Peter Obi baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiya mai suna Save Democracy Mega Alliance (SDMA), ta mika kokon bararta ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan zaben shekarar 2027.

Kungiyar ta bukaci Atiku da ya hakura da yin takarar shugaban kasa a zaben 2027, don marawa Peter Obi na jam'iyyar LP baya.

Ta bukaci Atiku ya karɓi matsayin jagora ɗan kishin kasa, kuma dattijo mai hangen nesa, ta hanyar marawa Peter Obi baya ya zama ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng