2027: Masoyin Ganduje Ya Faɗi Abin da Kano, 'Yan Arewa Za Su Yiwa Tinubu

2027: Masoyin Ganduje Ya Faɗi Abin da Kano, 'Yan Arewa Za Su Yiwa Tinubu

  • Wani na kusa da tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana yadda yan Arewa za su sakawa Bola Tinubu
  • Malam Umar Idris Shuaibu, ya ce Arewa, musamman Kano, za ta mara wa Tinubu baya a zaben 2027 saboda ayyukan alheri da ya yi
  • Shuaibu ya jinjina wa Ganduje bisa jagorancinsa na haɗin kai da karawa APC ƙarfi a Arewa, duk da rashin mulki a Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani kusa kuma masoyin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yaba masa kan kokarin da ya yi a APC.

Malam Umar Idris Shuaibu, ya bayyana tabbacin cewa Arewa za ta maida wa Bola Tinubu alherin sa da ƙuri’u masu yawa a zaben 2027.

Na kusa da Ganduje ya ce Arewa za su sakawa Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Abdullahi Ganduje yayin taro a Abuja. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

A wata tattaunawa da Punch a Kano, Shuaibu ya ce dangantakar Tinubu da shugabannin Arewa, tare da tawali’un Ganduje, sun haɗa APC sosai a yankin.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fadi abin alherin Tinubu ga Arewa

Shuaibu ya yaba wa Tinubu bisa kusanci da shugabannin Arewa, yana mai cewa shugaban ya yi wa Arewa abin alheri.

Jigon APC ya bayyana cewa ƙarfin siyasa da halin haƙuri na Ganduje ne ginshiƙin da ya sa APC ta ci gaba da zama mai ƙarfi a Kano.

Ya tuna cewa lokacin da Abdullahi Ganduje ya zama shugaban APC a watan Agusta 2023, jam’iyyar na cikin rikici, amma ya haɗa dukkan ɓangarori cikin ɗan lokaci.

“Dr. Ganduje mutum ne mai natsuwa, mai son mutane kuma mai yafiya. Saboda haka jam’iyyar APC tana ƙara ƙarfafawa ƙarƙashin tasirinsa.
“Da ya hau shugabanci, akwai rabuwar kai a APC,” in ji shi, “amma ya sulhunta, ya dawo da haɗin kai da yarda da juna.”

- Umar Idris Shuaibu

Ya ce, duk da cewa APC ba ta kan mulki a Kano, tsarin Ganduje da kulawa da magoya baya ya sa jam’iyyar ta tsaya da ƙarfi.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

An bayyana yadda Ganduje ya ba da gudunmawa a APC
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje a Abuja. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Facebook

An yabawa dan Ganduje saboda taimakon al'umma

Shuaibu ya kuma yaba wa ɗan Ganduje, Abba, bisa shirye-shiryen tallafi da taimako ga mambobin jam’iyya da suka ƙara ƙarfafa APC a jihar.

A ƙarshe, Shuaibu ya jaddada cewa Kano da Arewa za su saka wa Tinubu da goyon baya, ƙuri’u, da ƙarfin siyasa a zaben 2027.

Sai dai wani masanin siyasa, Dr. Ahmed Dandago, ya gargadi magoya baya ka da su dogara da tsarin Ganduje kadai wajen nasarar 2027.

Dandago ya ƙara da cewa dole ne gwamnatin Tinubu ta magance matsalolin tattalin arziki da tsaro domin samun amincewar matasa da talakawa.

Tinubu ya hadu da Ganduje a taro

Kun ji cewa Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar Imo inda ya samu rakiyar jiga-jigan APC da sauran siyasa domin kaddamar da ayyuka.

Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsofaffin shugabannin APC biyu; Adams Oshiomhole da Abdullahi Umar Ganduje suna daga cikin mahalarta bikin.

Kara karanta wannan

'Jonathan, Atiku da Peter Obi ba za su iya doke Shugaba Tinubu a zaben 2027 ba'

Har ila yau, akwai gwamnonin jihohin APC, tare da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, wadanda suka halarci kaddamar da ayyukan da kuma ƙaddamar da littafi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.