Tinubu, Fubara Sun Dawo Najeriya ana Shirin Dawo da Gwamnan Ribas Kujerarsa
- Shugaba Bola Tinubu da dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara sun katse tafiyarsu zuwa ƙasashen waje
- Wannan ya biyo bayan shirin da ake yi na miƙa mulki ga Fubara domin dawo da mulkin dimokiraɗiyya a Ribas
- Tuni jami'in da ya kula da jihar bayan dakatar da Ɗibar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya fara shirye-shiryen mika mulki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Rivers – Shugaba Bola Tinubu da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, za su koma Najeriya yau Talata.
Matakin ya zo a daidai lokacin da ake shirin kammala mulkin rikon kwarya da Shugaba Tinubu ya kakaba wa jihar a ranar Alhamis.

Source: Twitter
Sanarwara Hadimin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X ta ce Tinubu, wanda ya tafi hutu zuwa Faransa da Birtaniya tun ranar 4 ga Satumba, ya kammala hutunsa da wuri.
Bola Tinubu zai komo Najeriya
Jaridar Punch ta ruwaito cewar mashawarcin Shugaban Kasa a kan harkokin labarai, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai koma ofishinsa bayan ya sauka a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da yake birnin Paris, Tinubu ya gana da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée.
Taron ya tattauna kan dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa tare da shirin ƙara haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.
Tinubu: Ana shirin mika mulki a Ribas
Yanzu haka, hankula sun karkata kan shirin mika mulki wanda zai kawo ƙarshen mulkin soja na wucin gadi da Tinubu ya sa a jihar.
Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, wanda ya shugabanci jihar a lokacin dokar ta-baci, ya fara tsari da bikin godiya a Fatakwal ranar Lahadi.
Haka kuma, an shirya gabatar da lacca ta musamman a Fadar Gwamnati yau Talata, 16 ga Satumba, mai taken “Dimokuraɗiyya da Kyakkyawan Mulki”.

Source: Instagram
Ibas ne za a girmama a wajen taron, tare da fitattun baƙi da aka gayyata tun kafin ƙarfe 9:30 na safe.
Ana kuma sa ran Fubara, wanda ya dade a Landan, zai dawo yau Talata, bayan jinkirin da ya hana shi dawowa a ranar Litinin.
Wani makusancinsa ya shaida wa jaridar cewa:
“Gwamna zai dawo a ranar Talata kafin a dawo da shi ofis a ranar Alhamis, 18 ga Satumba.
Dawowar Tinubu zuwa Abuja da kuma Fubara zuwa Ribas ya ƙara jawo hankalin ‘yan kasa kan sauyin siyasa da za a samu a ƴan kwanaki masu zuwa.
Fubara zai koma kan mulkin jihar Ribas
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Rivers ta tabbatar da cewa ta fara shirin dawo da mulkin dimokuraɗiyya bayan watanni tana karkashin dokar ta-baci.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Ibibia Lucky Worika, ya fitar a ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar zai dawo kujerarsa a makon nan, bayan shafe watanni a waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

