‘Wanda Ya Kamata Ya Zama Ɗan Takarar ADC tsakanin Atiku, Obi da Amaechi’

‘Wanda Ya Kamata Ya Zama Ɗan Takarar ADC tsakanin Atiku, Obi da Amaechi’

  • An shawarci jam'iyyar ADC kan dan takarar da za ta fitar domin samun nasara a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Wata lauya, Titilope Anifowoshe, ta shawarci kawancen ADC da su fitar da dan takara mai gaskiya da kwarjini ga matasa
  • An bayyana cewa kawancen na son karbe mulki daga hannun Bola Tinubu a 2027, inda Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi ke sahun gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

An gargadi jam'iyyar hadaka ta ADC kan duba dan takarar da ya dace domin tsaya mata a zaben da ake tunkara na shekarar 2027.

Wata lauya mai suna Titilope Anifowoshe ta yi kira ga kawancen ADC da su zabi dan takarar shugaban kasa da yake da karbuwa a kasa baki daya.

An shawarci kan cire dan takara a 2027
An bukaci ADC ta zabi dan takara mai kyau tsakanin Atiku, Obi, Amaechi. Hoto: @Imranmuhdz.
Source: Twitter

'Dan takarar da ya kamata ADC ta cire tsaida'

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun huro wuta, suna so Dauda Lawal ya sauka daga kujerar gwamna

Ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da Legit.ng inda ta ce dole ne a zabi mutum mai tarihi mai kyau a shugabanci da hidimar jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anifowoshe ta bayyana cewa irin wannan dan takara zai zama abin karbuwa ga matasa, kuma ya zama mai kishin kasa da tunani na gyara al'umma.

Ta kara da cewa Najeriya tana bukatar kawance mai hangen nesa da hadin kai ba wai kawai neman cin zabe ba.

A cewarta:

“Idan burin su shi ne su fitar da dan takara mai cancanta, tsabta da karbuwa, sai su mai da hankali kan tarihi da kamun kai.”

Ta ce irin dan takarar da ake nema shi ne wanda zai hada kishin kasa, fahimta, jajircewa da matakin siyasa mai ma’ana da mutunci.

A halin yanzu dai kawancen jam’iyyun adawa ya rungumi ADC a matsayin dandalin siyasar su, wanda Atiku Abubakar ya fara jagoranta.

An hasashen Atiku, Obi da Amaechi suna sha'awar takara a 2027
An ba ADC shawara su duna nagartacce tsakanin Atiku, Obi da Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Shawarar da aka ba ADC game da 2027

Atiku ya bukaci shugabannin adawa da su hada kai domin karbe mulki daga wajen Bola Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Za mu shiga Aso Rock': Atiku ya fadi babban shirin ADC na karbar mulki a 2027

Peter Obi da Rotimi Amaechi suma sun nuna sha’awar tikitin takarar shugaban kasa karkashin ADC a zaben mai zuwa.

An kuma shawarci jam'iyyar ADC da ka da ta rika amfani da abubuwan da suka faru kamar jana’izar Muhammadu Buhari don samun karbuwa a wajen jama’a.

Lauyar ta ce Najeriya tana bukatar shugaba mai fahimtar bukatun zamani, wanda zai kawo hadin kai da ci gaban kasa.

Ta jaddada cewa bai kamata a zabi wanda ya fi hayaniya ba, sai dai wanda ya fi mutunci da dacewa da zamanin yanzu.

Atiku ya fadi shirin ADC a zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar ADC za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027 tare da karɓar mulki daga hannun APC.

Atiku ya ce ADC na da tsayayyen tsari da akida don ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki.

Tsofaffin jiga-jigan APC, PDP da kuma SDP sun koma ADC, yayin da aka nada sababbin shugabannin jam'iyyar a jihar Ekiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.