Gwamna Ya Buƙaci Atiku da Peter Obi Su Janye Burinsu na Takara a Zaben 2027
- Gwamnan Ondo ya buƙaci Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ƴan adawa su haƙura, su janye burinsu na neman shugabancin ƙasa a 2027
- Hon. Lucky Aiyedatiwa ya shawarci duka ƴan adawa su marawa kudirin tazarcen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓe mai zuwa
- Ya kuma buƙaci jama'ar jihar Ekiti su kara godewa Allah da ya ba su gwamna mai hangen nesa, wanda ya kawo masu ci gaba gagara misali
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ekiti - Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bukaci Atiku Abubakar da Peter Obi da su ajiye burinsu na takara su goyi bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Aiyedatiwa faɗi haka ne yayin da yake jawabi a gangamin APC da aka shirya a Ado Ekiti domin nuna goyon baya ga takwaransa na Jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji.

Kara karanta wannan
Fayose: Tsohon gwamnan PDP ya yi karatun ta natsu, ya fadi dalilin da zai sa Tinubu ya zarce

Source: Facebook
Gwamnan ya ce Tinubu zai samu nasara cikin sauƙi kuma zai dawo wa’adi na biyu a zaben 2027, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba jagororin adawa ƙarƙashin jagoranci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar sun haɗa kawance domin karɓe mulki daga hannun APC a 2027.
Gwamnoni 23 na tare da Shugaba Tinubu
Sai dai Aiyedatiwa ya bayyana cewa dukkan gwamnonin 23 na jam’iyya mai mulki watau APC suna goyon bayan mai girma shugaban ƙasa, ya ce hakan kaɗai nasara ce babba.
Lucky Aiyedatiwa ya jaddada da cewa tuni suka fara aiki a Kudu maso Yamma don tabbatar da ɗorewar mulkin Renewed Hope zuwa wa'adi na biyu a shekarar 2027.
Gwamnan Ondo ya bayyana Oyebanji, wanda ake yi wa lakabi da BAO, a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda ayyukansa da manufofinsa na ci gaba suka karaɗe ko’ina a faɗin Jihar Ekiti.

Kara karanta wannan
Tinubu: An yi hasashen wanda zai zo na 1, na 2, na 3 da na 4 a zaɓen shugaban ƙasar 2027
Ya ce mutanen Ekiti sun yi sa’a da samun gwamna mai irin wannan jajircewa, inda ya bukaci su sake ba shi dama ta biyu domin ya ɗora daga nasarorin da ya riga ya samu.
Gwamna Aiyeɗatiwa ya yiwa Oyebanji kamfe
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan Ondo, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook, Aiyedatiwa ya ce:
“Ekiti ta yi sa’a da samun BAO a matsayin gwamna. Ayyukan ci gaba da ke gudana a faɗin jihar a bayyane suke kuma abin a yaba ne, don haka ya cancanci wa’adi na biyu.”

Source: Facebook
Haka kuma, ya bukaci mambobin APC da sauran masu ruwa da tsaki da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Gwamna Oyebanji a dukkanin kananan hukumomi 16 da ke Jihar Ekiti.
Ya buƙaci yan APC su tabbatar da nasarar da jam’iyyar kamar yadda ya faru a zaɓen gwamna na 2024 a Jihar Ondo, inda APC ta ci dukkan kananan hukumomi 18.
Gwamna Oyebanji ya gargaɗi ƴan siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Oyebanji ya nuna damuwa kan saƙonnin da wasu ƴan siyasa ke tura masa suna nuna masa akwai matsala a shirinsa na tazarce a Ekiti.

Kara karanta wannan
Bayan tafiyar Atiku, an yi hasashen matsayi da PDP za ta ƙare a sakamakon zaɓen 2027
Gwamna Oyebanji ya bayyana cewa ba zai hana idonsa barci ba saboda kawai yana neman al'ummar Ekiti su sake zaɓensa a karo na biyu a 2026.
Ya buƙaci ‘yan siyasa su daina aika masa irin wadannan sakonnin ta wayar tarho domin hankalinsa na kan shugabanci da cika alƙawurran da ya ɗauka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng