Bayan Komawa APC, Ƴan PDP Sun Kunyata Ɗan Majalisa, Sun Ƙi Karbar Tallafinsa

Bayan Komawa APC, Ƴan PDP Sun Kunyata Ɗan Majalisa, Sun Ƙi Karbar Tallafinsa

  • Mambobin jam’iyyar PDP a Idanre, jihar Ondo, sun yi fatali da shirin tallafi da Hon. Festus Akingbaso ya shirya bayan sauya shekarsa
  • Shugaban PDP na Idanre, Ade Akinlalu, ya ce Akingbaso ya ci amanar al’umma kuma yana kokarin amfani da tallafi don jawo mambobi APC
  • PDP ta bayyana cewa ficewar Akingbaso ba za ta shafi karfinta ba, tana mai cewa Idanre har yanzu gida ne na jam’iyya mai alamar lema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Idanre, Ondo - Mambobin jam'iyyar PDP a jihar Ondo sun ba ɗan majalisar wakilai da ke wakiltarsu kunya.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Idanre ta jihar inda suka yi fatali da tallafin da ya ba su.

An watsawa ɗan majalisa ƙasa a ido
Dan majalisa ya ga ta kansa a Ondo. Hoto: Hon. Festus Akingbaso.
Asali: Facebook

An watsawa ɗan majalisar Ondo ƙasa a ido

Tribune ta ce Mambobin jam'iyyar sun yi watsi da tallafin Hon. Festus Akingbaso saboda ya koma APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar ya shirya hakan ne domin taimakon mambobin jam'iyyar a yankin saboda morar mulkin dimukraɗiyya.

Mambobin jam’iyyar, wadanda suka bayyana shirin a matsayin na yaudara kuma na siyasa, sun ce lokaci bai yi ba kuma ba su amince da wannan yunƙuri ba.

Martanin shugabannin PDP kan lamarin

Shugabannin jam’iyyar sun ce shirin tallafin wani yunkuri ne na jan hankalin mambobin PDP zuwa APC da kyaututtuka daga dan majalisar da ya sauya sheka.

Da yake magana, shugaban PDP a karamar hukumar Idanre, Hon. Adekunle Akinlalu, ya nuna bacin ransa da abin da ya faru.

Akinlalu ya ce Akingbaso ya gane cewa ya koma jam’iyyar da ta mutu murus wacce ba za ta sake tasiri ba.

A cewarsa, Akingbaso ya ci amanar mutanen da suka zabe shi, kuma ya kunyata al’ummar da suka gaskata kwarewarsa da nagartarsa.

Akinlalu ya bayyana cewa PDP na ganin shirin tallafin wata hanya ce ta neman farin jini, inda ya ce kayan da ake rabawa na cikin kasafin kudin 2024 ne.

Ya ce bai fahimci dalilin sauya shekar Akingbaso ba, bayan samun nasarar tsayawa takara da lashe zabe a kujeru daban-daban a jam’iyyar PDP.

Yan PDP sun ƙi karbar tallafi daga ɗan majalisa
Mambobin PDP sun yi fatali da tallafin dan majalisa. Hoto: Legit.
Asali: Original

PDP ta fadi karfin da jam'iyyar ke da shi

Wani jigo a jam’iyyar a karamar hukumar, Mayokun Akinmoladun, ya ce taron ya zama dole don bayyana cewa sauya shekar Akingbaso ba zai shafi PDP ba.

“PDP jam’iyya ce mai ƙarfi. Ficewarsa ba ta shafi komai game da jam’iyyar. Duk wata harka na tafiya yadda ya kamata.
“Mun amince da PDP saboda tunaninta na ci gaba. Tun zamanin Gwamna Agagu, PDP ta kawo ci gaba sosai a garinmu.

- Cewar jigon PDP

Ɗalibai sun ƙi karbar shinkafar Tinubu

A baya kun ji cewa shugabannin daliban jami'ar ABU da ta OAU sun yi watsi da tallafin shinkafa da gwamnatin Bola Tinubu ta ba su.

Daliban sun bayyana cewa wannan ba zai magance matsalolin ilimi da ya dabaibaye manyan makarantu ba.

Gwamnatin tarayya ta ware buhunan shinkafa ga shugabannin kowace jami'a, kwalejin fasaha da ta kimiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.