Gwamnatin Kano Ta Rufe Makarantu, Ta Bayyana Ranakun Komawa
- Gwamnatin jihar Kano ta hannun ma'aikatar ilmi ta bayar da hutun Sallar Layya ga dukkanin makarantun firamare da sakandire
- Ma'aikatar ilmi ta jihar Kano ta bayyana cewa hutun babbar sallar ya shafi dalibai da ke a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu
- Hakazalika, a cikin sanarwar da Ma'aikatar ilmin ta fitar ta bukaci iyayen yara da su tabbatar da cewa yaransu sun dawo makaranta a ranar da ake komawa hutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun ma'aikatar ilmi, ta sanar da hutun Sallar Layya (Eid-el-Kabir) ga makarantu a fadin jihar.
Ma'aikatar ilmin ta Kano ta bayar da hutun ga makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da darakta mai kula da wayar da kan jama’a na ma'aikatar ilmi ta jihar Kano, Misbahu Yakasai, ya fitar ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano
Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutu
Bisa ga umarnin bayar da hutun, dukkan makarantun kwana za su tafi hutu ne daga ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, kuma za su dawo ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026.
Haka zalika, makarantun je ka-ka-dawo za su fara hutun na Sallah ne daga ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, 2026, kuma za su dawo ranar Litinin, 1 ga watan Juni, 2026.
An ba iyaye shawara
Sanarwar ta buƙaci iyaye da masu riƙon ɗalibai da su ɗauki yayansu a ranar da za a rufe, kuma su tabbatar da sun dawo a kan lokaci a ranar da za a koma, jaridar Tribune ta kawo rahoton.
“Ana shawartar iyaye da masu riƙon ɗalibai na makarantun kwana da su ɗauki yayansu a ranar rufewa da aka amince da ita, wato Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, kuma su tabbatar da sun dawo akan lokaci a ranar komawa."
- Misbahu Yakasai

Source: Original
Kwamishinan ilmi ya taya iyaye murnar sallah
Kwamishinan ilmi, Dr. Ali Makoda, ya yi wa ɗalibai, malamai, iyaye, da daukacin mutanen da ke a fannin ilimi fatan gudanar da bukukuwan Sallar Layya lafiya cikin farin ciki.
Bayar da hutun dai na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da babbar Sallah a Najeriya da sauran kasashe.
Gwamna Abba ya zama dan takarar APC a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zama dan takara daya tilo mai neman kujerar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar APC ta amince da Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin tsayawa takarar wa’adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Amincewar ta biyo bayan nasarar da gwamnan ya samu a gaban kwamitin ayyuka na ƙasa na APC bayan ya miƙa fam ɗin tsayawa takara da na tantancewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
