'Hanya 1 da 'Yan Adawa Za Su Bi domin Kayar da Tinubu a 2027,' Inji Dele Momodu

'Hanya 1 da 'Yan Adawa Za Su Bi domin Kayar da Tinubu a 2027,' Inji Dele Momodu

  • Dele Momodu ya bayyana cewa haɗin kan jam'iyyun adawa kaɗai zai iya kwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Ya bayyana rashin jin daɗinsa da halin da PDP ke ciki yanzu, inda ya ce ruhinsa ya dade da barin jam'iyyar, jikinsa ne kawai ke tare da ita
  • Momodu ya ce APC na tsoron PDP a matsayin jam'iyyar adawa mafi ƙarfi, don haka suke ƙoƙarin rura wutar rikici domin raunana ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dele Momodu, wanda ya taɓa neman shugabancin ƙasa sau biyu kuma jigo ne a jam'iyyar PDP, a ranar Talata ya yi magana kan zaben 2027.

Dele Momodu ya bayyana cewa haɗin kan jam'iyyun adawa ne kaɗai zai iya kwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a 2027.

Dele Momodu ya ba 'yan adawa sirrin kayar da Tinubu a zaben 2027
Dele Momodu tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @DeleMomodu
Asali: Facebook

Dele Momodu ya fadi hanyar nasarar PDP

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a cikin shirin "bakon wata" na gidan rediyon BCOS da ke Oyo, wanda yake a Ibadan, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya bayyana cewa "Ruhina ya riga ya bar PDP, jikina ne kawai ya rage a jam'iyyar," wanda ke nuni da rashin gamsuwarsa da halin da jam'iyyar ke ciki a halin yanzu.

Ya ci gaba da cewa:

"Idan har PDP za ta shiga haɗaka, to tana da duk abin da ake buƙata don kwace mulki daga hannun APC a 2027, amma abubuwan da ke faruwa ba za su bari hakan ta faru ba."

"APC na tsoron jam'iyyar PDP" - Dele Momodu

Dele Momodu ya bayyana cewa APC tana tsoron PDP, inda ya lura cewa ita ce kaɗai jam'iyyar adawa mai ƙarfi da za ta iya kalubalantar ikon ta a 2027.

"Wannan ne ɗaya daga cikin dalilan da ya sa shugabannin APC a kowane mataki ke kokarin ganin cewa jam'iyyar PDP ba ta fita daga rikicin da take ciki ba."

- Dele Momodu.

Ya jaddada cewa:"Babu yadda za a yi PDP da ba ta da haɗin kai ta kwace mulki daga APC a 2027," yana mai cewa manufar jam'iyya mai mulki ita ce ta raunana babbar jam'iyyar adawa.

Wani babban kalubalen kuma, a cewarsa, shi ne rikicin cikin gida a PDP, ya ce "ana amfani da wasu daga cikin mambobinta don yi mata zagon kasa tare da hana ta sakat."

Dele Momodu ya ba yan adawa shawarar fito da dan takarar shugaban kasa daga Arewa
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu. Hoto: @DeleMomodu
Asali: Facebook

Momodu ya magantu kan tunbuke Tinubu a 2027

Duk da haka, jaridar Punch ta rahoto Momodu ya bayyana cewa:

"PDP jam'iyya ce mai bin doka. Kullum tana bin tsarin da ya dace kafin yanke kowane irin hukunci kan mambobinta."

Momodu ya ci gaba da bayanin cewa abu ne mai wahala a tunbuke Shugaba Tinubu ba a 2027, har sai idan an samu hadakar jam'iyyun adawa.

"Duk wanda zai fafata da shugaban ƙasa mai ci dole ne ya fito daga wani yanki daban da na shugaban ƙasar, wannan ne hanyar warware rikici kan fito da dan takara."

- Dele Momodu.

"Ana yaudarar Shugaba Tinubu" - Dele Momodu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dele Momodu, ya bayyana cewa al'ummar Najeriya na fama da matsaloli a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu yanzu.

Momodu ya nuna damuwa cewa Shugaba Tinubu na iya fassara sauya sheƙar da wasu ƴan siyasa ke yi zuwa jam'iyyar APC a matsayin alamar nasarar gwamnatinsa a kasar.

Sai dai a cewarsa, ana yaudarar Tinubu ne kawai da wadannan alkaluma na sauya sheka, yana mai nuna muhimmancin amfani da tattalin arziki matsayin ma'aunin ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.