'Jam'iyya 1 ba za Ta Iya ba,' Tsohon Dan Takara Ya Fadi yadda za a Kwace Mulki daga Tinubu
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a NCP, Martin Onovo ya bayyana cewa akwai hanyar da za a iya kawar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Cif Martin Onovo ya bayyana haka ne a lokacin da Atiku Abubakar da wasu yan adawa ke kokarin hada hadakar da za ta kifar da gwamnati
- Ya ce matukar aka hada kai da gaske, babu wata barazana da jam'iyyar APC mai mulki za ta yiwa yan adawa a filin babban zaben 2027 mai zuwa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NCP da aka rushe a 2015, Cif Martin Onovo, ya ce zai yi wahala jam’iyyar adawa guda daya ta iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Onovo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi kan makomar sauran jam'iyyun adawa yayin da ake fafutukar kwace mulki daga hannun gwamnatin APC.

Asali: Twitter
Jaridar The Nation ta wallafa cewa tsohon dan takarar na ganin babbar hanya daya tilo da za a iya kayar da jam’iyyar APC ita ce ta hanyar hadin gwiwar jam’iyyun adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda za a kifar da gwamnatin Tinubu
Jaridar Punch News ta ruwaito cewa Onovo ya yabawa yunkurin tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da wasu shugabannin siyasa na kafa hadakar adawa.
Ya ce:
“Ni ne na jagoranci hadakar siyasa mafi girma a wannan jamhuriya wato CUPP, kuma zan iya tabbatar da cewa hadaka ce kadai mafita."
“Idan ba su bata rawarsu da tsallensu da yawa, hadakar za ta ci zabe da 99% a 2027. Ku rubuta wannan, idan an yi shi da kyau, za su ci zabe da rinjaye.”
Tsohon dan takaran ya soki gwamnatin Tinubu
Dangane da ayyukan gwamnatin Tinubu, Onovo ya nuna rashin gamsuwa da abin da aka cimma, musamman a bangaren tsaro da samar da bukatu na yau da kullum ga talakawa.
Ya shawarci Shugaba Tinubu da ya yi amfani da shekarun da suka rage a wa’adinsa na farko wajen magance matsalolin tsaro da inganta rayuwar al’umma.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Shugaban kasa ya bayyana manufofinsa, amma ya kamata ya dage wajen kyautata walwala da tsaron rayukan ‘yan Najeriya a birane da kauyuka.
“Muna bukatar kwararru a mukamai, ba masu yi masa biyayya kawai ba. A kawo dabarun da suka dace, a gina tsari mai tsafta."
Ndume ya ki goyon bayan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Ali Ndume ya bayyana rashin goyon bayansa ga kudurin gwamnonin APC na goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya sake tsayawa takara a zaben 2027.
Ndume ya bayyana cewa ya halarci taron koli na gwamnonin APC 22 a fadar shugaban kasa, amma lokacin da aka fara tattaunawa kan goyon bayan Tinubu don tazarce, sai ya fice daga taron.
Sanata Ndume ya ambaci cewa duk da goyon bayan gwamnonin PDP ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben 2015, hakan bai hana shi faduwa babban zaben ba.
Asali: Legit.ng