Sheikh Kabiru Gombe Ya Faɗi Maƙarƙashiyar da Ƴan Siyasa Ke Yiwa Malamai
- Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya zargi ‘yan siyasa da shirya farfaganda kan malamai saboda tsoron tasirinsu a siyasa
- Shehin malamin ya bayyana cewa ana kokarin bata sunan malamai a idon talakawa domin hana su jin maganasu
- Malamin Izalan ya ce kundin tsarin mulki bai ba malamai hakkin bibiyar gwamnati ba, sai dai ‘yan majalisa da sanatoci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi magana kan halayen yan siyasa.
Shehin malamin ya fadi abubuwan da yan siyasa ke shiryawa malamai saboda tsoron tasirinsu da suke yi a rayuwarsu.

Asali: Facebook
Zagin malamai: Kabiru Gombe ya zargi 'yan siyasa
Sheikh Kabiru Gombe ya fadi haka ne yayin hira da gidan jaridar DCL Hausa da ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Najeriya da dama na yawan zagin malamai musamman duk lokacin da wani dan siyasa ya gaza yin abin da ya dace.
Malamai da dama na yawan jan kunne kan haka ganin cewa su ne magada Annabawa da suke kokarin kai al'umma tudun na tsira.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce kana ganin yadda ake sukar malamai ka san kawai farfaganda ce ta yan siyasa da suke neman ruguza su.
Sakataren kungiyar Izalah ya jaddada cewa malamai suna da tasiri a cikin al'umma shiyasa ake neman hada su da talakawa.
A cewarsa:
"Meyasa kullum malamai, malamai a bakin mutane, ba wani abu ne illa yan siyasa suna tsoron tasirin malamai a siyasa.
"Suna ganin cewa za su kwace musu damar kafa shugabanni akwai lokacin da yan siyasar ba su da tasirin kafa shugabanni.
"Su kuma yan siyasar nan ba su da sana'a ba abin da suka sani sai wannan harka, su samu ofis su debi kudin jama'a su yi abin da suka ga dama."

Asali: UGC
Kabiru Gombe ya fadi nufin yan siyasa
Kabiru Gombe ya ce yan siyasa sun shirya hakan ne domin hada malaman da talakawa saboda su ci karensu ba babbaka.
Ya ce:
"To ya ya za su yi su bata malaman a fuskar talakawa yadda za su bar sauraronsu saboda su ci gaba da cin karensu babu babbaka.
"Wannan kawai shi ne shirin da aka yi a Najeriya, idan ka kalli surutun da ake kan malamai ba sai an fada maka ba.
"Kana gani ka san farfaganda ne, malaman nan ba su ne ministoci ko kwamishinoni ko gwamnoni ko yan majalisu ko Sanatoci ba."
Malamin ya ce a kundin tsarin mulki sanatoci da yan majalisu ne ke da hakkin bibiyar kuskuren gwamnatoci ba malamai ba.
Kabiru Gombe ya magantu kan zaben shugabanni
A wani labarin mai kama da wannan, Sheikh Kabiru Gombe ya yi magana kan sukar malamai da ake yi kan zaluncin shugabanni.
Shehin ya bayyana cewa talakawa su ne ke zaben azzaluman shugabanni ta hanyar karɓar kudi daga ‘yan siyasa lokacin zaɓe.
Malamin ya ce malamai ba su da ikon tsayar da ɗan takara, domin jam’iyyu ne ke da wannan damar, ba kungiyoyin addini ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng