Sheikh Kabiru Gombe Ya Kare Malamai kan Zaben Rubabbun Shugabanni a Najeriya
- Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa talakawa su ne ke zaben azzaluman shugabanni ta hanyar karɓar kudi daga ‘yan siyasa lokacin zaɓe
- Ya ce malamai ba su da ikon tsayar da ɗan takara, domin jam’iyyu ne ke da wannan damar, ba kungiyoyin addini kamar Izala ba
- Malamin addinin ya ƙara da cewa ba daidai ba ne a zargi malamai idan shugabannin da aka zaɓa sun lalace, alhali ba su tsayar da su ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya yi tsokaci kan zaben azzaluman shugabanni a Najeriya da ake ta fama da su.
Malamin ya fadi rawar da malamai suke takawa wurin tabbatar da zaben shugabanni nagari a lokacin zabe.

Asali: Facebook
Kabiru Gombe da zaben azzaluman shugabanni
Shehin ya fadi haka ne yayin hira da jaridar DCL Hausa da ta wallafa a shafin Facebook a safiyar yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Kabiru Gombe ya ce ya kamata al'umma su gane malamai ba su da tasiri wurin zaben yan takara tun farko saboda hakkin daliget ne na jam'iyya.
Ya ce babu dadi kwata-kwata yadda mutane suke sukar malamai bayan kuma ba su da damar tsayar da dan takara a kasa ko a jihohi.
Ya ce:
"Mutane su fahimci cewa a lokacin da ake zaben shugabannin nan fa, daliget da ake daukowa daga cikin talakawa a yi taro a ba su kudi.
"Daliget din ne su ke zaben shugaban da bai dace ba saboda sun karbi kudin gwamnati a tsayar da su takara.
"Su malaman sai dai su ga an tsayar da dan takara, kuma yan takarar nan za ka ga babu wanda ya cancanta idan ma'auni na addinin Musulunci za ka duba."

Asali: UGC
Zaben shugabanni: Kabiru Gombe ya shawarci alumma
Malam Kabiru Gombe ya ce asalin wadanda ke zabar shugabanni azzalumai talakawa ne bayan an biya su makudan kudi.
Ya ce amma abin takaici al'umma sai su daurawa malamai laifi kamar su ne suka nada yan takara a jam'iyyun siyasa.
Ya kara da cewa:
"Amma asalin wadanda suka zabi yan takarar da ake nadawa ba malamai ba ne ke tsaida su ba, babu damar tsayar da dan takara sai da jam'iyya.
"Yanzu duk yawanmu a kungiyar Izalah babu yadda za mu tsayar da dan takara saboda ba jam'iyya ba ce, dole sai da jam'iyya za ka tsayar da dan takara.
"Amma bayan ba su kudi sun tsayar da dan takara ya zo yana abin da bai dace ba sai kuma a zo ana zagin malamai ba su masa wa'azi ba ko nasiha ba."
Kabiru Gombe ya soki salon mulkin Tinubu
Kun ji cewa Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya yi magana kan zargin da ake yi wa malamai cewa suna ci da addini a Najeriya.
Malamin ya yi bankada, ya ce ainihin masu ci da addini ba su wuce Bola Tinubu da Kashim Shettima da kuma mukarrabansu ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ganin Sheikh Sani Yahaya Jingie na kokarin kare muradun gwamnatin Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng