Abin da Ya Sa Ɗan Sanda Ya Durƙusa gaban Ganduje, Ya Ɗaure Masa Takalmi a Bidiyo
- Aminu Ɗahiru Ahmad, hadimin shugaban APC ya karyata maganganun da ake yaɗawa kan bidiyon ɗan sandan da ya ɗaurewa Abdullahi Ganduje takalmi
- Aminu, mai kula da harkokin ɗaukar hoto a ofishin shugaban APC na kasa ya ce mutuntawa ce ta sa ɗan sandan ya yi hakan
- Ya ce duk wanda ya san tsohon gwamnan na Kano, ya san mutum ne wanda ke girmama duka waɗanda ke aiki a ƙarƙashinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hadimin shugaban APC na ƙasa, Aminu Dahiru Ahmad ya kare ɗan sandan da aka gani a faifan bidiyo ya durƙusa ya gyara takalmin Abdullahi Ganduje.
Hadimin na Ganduje ya bayyana cewa abin da ɗan sandan ya yi kyautata wa ce kawai, ba wai cin mutuncin kayan ƴan sanda ba.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Aminu Ɗahiru ya zargi masu neman ɓata sunan shugaban APC da yaɗa wannan faifan bidiyo a kafafen sada zumunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ɗan sanda ya durƙusa gaban Ganduje
Tun farko dai wani faifan bidiyo da wani mai suna Chuks a taƙaice ya wallafa a shafin X, ya nuna wani ɗan sanda ya ɗaure igiyar takalmin Ganduje.
Bidiyon ya nuna yadda ɗan sandan ya durƙusa kan gwiwarsa, sannan ya yi wani ɗan gyara da bai wuce ɗaure igiyar takalmin shugaban APC na ƙasa, Ganduje ba.
Lamarin ya ja hankalin ƴan Najeriya musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, wasu na ganin abin da ɗan sandan ya yi cin mutuncin jami'an tsaro.
Hadimin Ganduje ya kare ɗan sandan
Da yake martani, Aminu Ɗahiru Ahmad ya ce wasu masu neman ɓata Ganduje ne suke yaɗa faifan bidiyon tare da gurbatattun kalamai.
Hadimin ya kara da cewa masu hannu a ƙoƙarin ɓata shugaban APC suna haka ne saboda sun firgita da nasarorin da yake samu a baya-bayan nan.
Ya ce abin da ya faru na da tushe bisa “shaidar da aka samu daga ganau” waɗanda suka tabbatar da cewa ɗan sanda ya gyarawa Ganduje takalmi ne saboda kulawa da tsaronsa.
“Wannan gajeren bidiyo shaida ne na yadda mu’amala ke tafiya cikin natsuwa da girmamawa tsakanin Dr Abdullahi Umar Ganduje da hadimansa.
"Duk wanda ya san Ganduje zai tabbatar da cewa yana ɗaya daga cikin jagororin siyasa mafi ladabi da mutunci a Najeriya.
Na shafe kusan shekara goma ina aiki da shi. Yana kula da ni kamar ɗansa na cikinsa.”
- In ji Aminu Ɗahiru Ahmad.

Asali: Twitter
'Abin da ya sa ake kokarin ɓata Ganduje'
Ya yi zargin cewa bidiyon ya fito ne daga hannun wasu da ke son haddasa rikici domin su cimma wata manufar siyasa, inda ya buƙaci jama’a su yi watsi da kalmomin da aka jinginawa Ganduje.
Hadimin shugaban APC ya ce:
"Tabbas wannan bidiyo ba zai rage farin jinin Ganduje ba. Ya riga ya yi wa al’ummar Kano aiki tukuru, kuma yanzu yana hidimtawa ƙasa baki ɗaya.
"Ƴan adawa ba su jin daɗin yadda Ganduje ke ƙara wa APC ƙarfi musamman ganin yadda Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da abokin takarar Atiku na 2023, Ifeanyi Okowa, suka sauya sheƙa zuwa APC.”
Ganduje ya faɗi shirin APC a zaben 2027
A wani labarin, kun ji cewa Ganduje ya ce APC na aiki da Majalisar Tarayya domin bai wa ƴan Najeriya mazauna kasashen ketare damar kaɗa kuri'a a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan Kano ya faɗi haka ne yayin kaddamar da shugabannin APC reshen kasar Faransa a birnin Faris.
Shugaban APC ya yabawa jagoorin jam'iyyar na kasashen waje bisa yadda suke ƙara tallata APC, tana kara yaɗuwa a tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng