'Ciwon Ido': Jigon PDP Ya Faɗi Mutane 2 da Za Su Zama Barazana ga Ƴan Adawa a 2027
- Babba a jam'iyyar PDP ya ce kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027 babban aiki ne, ya ce zaben zai yi kama da gasar cin kofin duniya
- Cif Dele Momodu ya soki gwamnonin PDP da suka ki shiga kawancen Atiku, Peter Obi da El-Rufai yana mai zarginsu da taimakawa APC
- 'Dan siyasar ya ce 'yan adawa suna cikin tsoro saboda Tinubu, ya nemi su dage da gwagwarmaya kuma su daina ficewa daga jam’iyyunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi gargadi ga masu shirin tsayawa takara a zaben 2027.
Dele Momodu ya gargadi 'yan adawar APC a 2027 da su sani cewa kalubalantar Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike 'jan aiki ne.'

Asali: Facebook
Jigon PDP ya gargadi 'yan adawa kan Tinubu
A wata hira da aka yi da shi a Arise Television, Dele Momodu ya yadda da ƙarfin siyasar Tinubu, wanda ko kafin ya zama shugaban ƙasa yana da ƙarfi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan siyasar ya ce sannan haɗuwar shugaban kasar da Nyesome Wike ta ƙara masa ƙaimi.
“Tinubu, wanda yanzu shi ne shugaban ƙasa, ya jima yana ba mu ciwon kai, tun ma kafin ya zama shugaban ƙasa, to balle kuma yanzu” inji Dele Momodu.
Jigon jam'iyyar na PDP ya kuma kara da cewa:
“Yanzu da Tinubu da Wike suke tare, ya zama babban kalubale ga wadanda ke son tsayawa takara a 2027, domin zaben shekarar zai zama tamkar gasar cin kofin duniya, dole ka fito da ‘yan wasa ƙwararru.”
An soki gwamnonin PDP kan kawancen hamayya
Momodu ya caccaki gwamnonin jam’iyyar PDP kan kin shiga kawancen hamayya da Atiku Abubakar ke jagoranta, yana cewa hakan zai iya taimakawa Tinubu ya yi nasara.

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya bugi kirji, ya fadi sabuwar jiha da gwamnatin Tinubu za ta kirkiro
Kawancen da ake kokarin samarwa ya haɗa da Atiku, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.
Sai dai bayan ganawarsu a Ibadan, gwamnonin PDP sun ce ba za su shiga wannan kawance na Atiku ba, kamar yadda muka ruwaito.
“Shugabannin hamayya sun daɗe suna kokarin hade kai. Gaskiya Atiku ba zai iya shi kaɗai ba, haka Peter Obi da Kwankwaso. Duk mai son takara sai sun haɗa kai, sannan su tunkari APC."
- Dele Momodu.
Kiran gwagwarmaya da haɗin kai

Asali: Original
Jaridar Vanguard ta rahoto kusan na jam'iyyar ta PDP ya bayyana damuwa kan tsoron da ke addabar 'yan hamayya, yana cewa:
“Yanzu dukkanmu mun koma kamar wata farar kura, ga tsoro ga ban tsoro. Kowa yana cikin tsoro saboda Tinubu, kowa na tsoron za a tura masa EFCC, ko za a kama shi.”
- Dele Momodu
Ya jaddada cewa dole ‘yan siyasar adawa su nuna jarumta, su daina fatan samun mulki cikin sauƙi, yana mai cewa duk wanda ya fice daga jam'iyyar adawa to yana cikin ruwa tsulundum.
'Har yanzu yana jin radadin 2023' - Momodu ga Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jigon PDP, Dele Momodu, ya ce har yanzu Nyesom Wike bai warke daga raunin da ya ji bayan faduwar da ya yi a zaben fidda gwani na 2023 ba.
Momodu ya ce Wike ya shigo zaben da yakinin dole sai ya samu tikitin takarar shugaban kasa, amma aka kayar da shi, lamarin da har yanzu ke damunsa.
Ana ganin Wike da sauran gwamnonin G5 sun taka muhimmiyar rawa wajen hana Atiku Abubakar samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng