Ana Batun Sauya Shekar El Rufai, Sabuwar Matsala Ta Taso Uba Sani a Kaduna
- Tsofaffin ma'aikatan da suka yi ritaya a Kaduna sun gaji da haƙuri kan halin da suka tsinci kansu sakamakon rashin biyansu haƙƙoƙinsu
- Ma'aikatan waɗanda suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata, 11 ga watan Maris 2025 a cikin birnin Kaduna
- Tsofaffin ma'aikatan da suke amfani da tsarin fansho na CPS, sun ba Gwamna Uba Sani wa'adin makonni biyu domin ya biya su haƙƙoƙinsu
- Sun bayyana cewa suna cikin wani hali sakamakon rashin samun kuɗi, inda suka ce mambobinsu da dama suka mutu saboda yunwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsofaffin ma'aikatan da suka yi ritaya da ke ƙarƙashin tsarin fansho na CPS sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna.
Tsoffafin ma'aikatan sun ba Gwamna Uba Sani, wa'adin kwanaki 14 domin ya biya su haƙƙoƙinsu.

Kara karanta wannan
Matasa sun fusata a watan azumi, sun ƙona fadar mai martaba sarki a Arewacin Najeriya

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsofaffin ma'aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Talata, 11 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsofaffin ma'aikata sun yi zanga a Kaduna
Tawagar tsofaffin ma'aikatan sun yi barazanar yin zaman dirshan a gidan gwamnatin jihar Kaduna, idan har ba a cika musu buƙatunsu ba a cikin mako biyu.
Shugaban tawagar, Farfesa Nate Danjuma wanda ya jagoranci zanga-zangar zuwa Sir Kashim Ibrahim House, ya bayyana cewa mambobinsu suna mutuwa saboda yunwa.
"Muna ba Gwamna Uba Sani wa’adin makonni biyu ya biya mu haƙƙoƙinmu, idan ba haka ba, za mu mamaye gidan gwamnati."
“Wasu daga cikin mambobinmu sun kamu da cututtukan hauka saboda rashin kula da lafiya, wasu sun mutu saboda yunwa, kullum muna rasa ƴan uwanmu. Wasu ba su iya biyan kuɗin asibiti. Wasu da dama sun rasa matsuguni."
“Mambobinmu sun samu nakasa, iyalanmu sun tarwatse, wasu na makancewa, muna fama da cututtuka kuma ba mu da kuɗin kula da kanmu da iyalanmu."

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
- Farfesa Nate Danjuma
Tsofaffin ma'aikatan Kaduna na shan wuya
Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan da suka yi magana sun bayyana halin da suke ciki, inda suka ce suna rayuwa da ƙyar, suna samun abinci cikin wahala.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna, CP Muhammad Rabiu, wanda ya yi magana da masu zanga-zangar, ya gode musu saboda gudanar da zanga-zangar cikin lumana.
Ya tabbatar musu da cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, zai duba koke-kokensu.
Gwamna Uba Sani ya sha alwashi a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana burin da yake da shi kan jihar kafin ya bar kujerar mulki.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa yana da aniyar ganin ya bar jihar Kaduna cikin yanayi mai kyau fiye da yadda ya same ta a lokacin da ya shiga ofis.
Uba Sani ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta maida hankali wajen samar da romon dimokuraɗiyya ga nutanen da suke rayuwa a cikin yankunan karkara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng