Jigawa: Rikicin APC Ya Sauya Salo, Majalisar Kansiloli Ta Tsige Ciyaman

Jigawa: Rikicin APC Ya Sauya Salo, Majalisar Kansiloli Ta Tsige Ciyaman

  • Kai ruwa rana a jam'iyyar APC ta Jigawa bai kare ba yayin da aka wayi gari da batun tsige shugaban karamar hukumar Ringim
  • Kakakin majalisar Kansilolin ne ya sanar da haka a wata sanarwa, yace kusan kowane Kansiƙa da ya hannu banda mutum ɗaya
  • APC ta samu matsala a Jigawa ne tun gabanin zaɓen fidda gwani na mazaɓar Jigawa ta arewa maso yamma

Jigawa - Rigingimun da suka hana jam'iyyar APC zaman lafiya a Jigawa sun bude sabon shafi ranar Litinin bayan tsige shugaban ƙaramar hukumar Ringim, Shehu Sule.

Shugaban majalisar Kansilolin Ringim, Badamasi Garba, mai wakiltar mazaɓar Gabi ne ya sanar da batun ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

APC a Jigawa.
Jigawa: Rikicin APC Ya Sauya Salo, Majalisar Kansiloli Ta Tsige Ciyaman Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Tsigaggen shugaban ƙaramar hukumar, Mista Sule, ana ganin yana cikin Ciyamomin yankin mazabar Jigawa ta arewa maso yamma waɗanda ke goyon bayan Sanata Danladi Sankara.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

Sanata Sankara mai wakilatar arewa maso yammacin Jigawa, ya ja daga da gwamna Muhammad Badaru ne tun kafin zaben fidda gwanin APC a shiyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sankara ya zargi gwamna Badaru da masa zagon ƙasa da nuna banbanci daga bisani kuma ya janye da shiga zaben, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A 'yan kwanakin da suka gabata aka hangi Sankara ya sa labule kofa kulle da Mustapha Lamido, ɗan takarar gwamnan Jigawa a inuwar PDP. Taron ya rikirkita wasu mambobin APC.

Ana ganin Tara daga cikin shugabannin kananan hukumo 12 da suka haɗa mazabar Sanatan duk suna goyon bayan Ɗanladi Sankara, wanda ya kauracewa duk wasu tarukan APC.

Meyasa majalisar Kansiloli ta tsige Ciyaman ɗin?

Garba, wanda ya yi jawabi a madadin Kansilolin Ringim, ya yi bayanin cewa ya sa hannu kan takardar ne bayan mafi rinjayen Kansiloli sun aamince da sauke Ciyaman ɗin.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakaru Sun Sheke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Yaransa 12 da Suka Addabi Jihohin Arewa 4

A cewarsa daga cikin Kansiloli 10 dake Ringim, Tijjani Rabo, Kansilan gundumar Sankara ne kaɗai bai rattaaɓa hannu kan takardar tsigewan ba.

A takardar, majalisar Kansilolin ta zargi Ciyaman da maida su saniyar ware ta hanyar ba da ayyukan kwangila ba tare da sahalewarsu ba.

Sule ya maida martani

Shugaban ƙaramar hukumar, wanda kujerarsa ke tangal-tangal, yace zai ɗauki mataki kan batun tsige shi a Lokacin da ya dace.

Idan baku manta ba a watan Mayu, majalisar dokokin Jigawa, ta sauke shugaban karamar hukumar Yankwashi, Mubarak Ahmad, wanda ɗan tsagin Sankara ne saboda ya yi korafin Deleget ɗin da gwamna ya zaɓa.

A wani labarin kuma Bayan Sauya Shekar Mambobin PDP, Fitacciyar Jam'iyya Ta Rushe Kanta, Ta Koma APC A Katsina

Ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar APC, Dakta Dikko Umaru Radda, na ci gaba da samun goyon bayan al'umma a wuraren yakin nemna zaɓensa.

Bayan mambobin PDP da NNPP dake tururuwar komawa APC, jam'iyyar PRP kacokan da rushe zuwa cikin jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Sauya Shekar Mambobin PDP, Fitacciyar Jam'iyya Ta Rushe Kanta, Ta Koma APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel