2027: Shugaban SDP Ya Gano Abin da Zai Hana Tinubu Sake Samun Nasara

2027: Shugaban SDP Ya Gano Abin da Zai Hana Tinubu Sake Samun Nasara

  • Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya fito ya nuna adawarsa ga manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Shehu Gabam ya bayyana cewa manufofin shugaban ƙasan kan tattalin arziƙi, na iya zama abin da zai sanya ya sha kaye a zaɓe
  • Shugaban na SDP ya kuma caccaki gwamnatin Tinubu kan yadda ta ɗauki karan tsana, ta ɗorawa ƴan adawa masu gaya mata gaskiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam, ya yi magana kan manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban na jam'iyyar SDP ya ce manufofin Tinubu kan tattalin arziƙi na iya zama babban kuskuren da zai hana shi samun nasara idan ya sake tsayawa takara a 2027.

Shugaban SDP ya caccaki manufofin Tinubu
Shehu Gabam ya soki manufofin gwamnatin Bola Tinubu Hoto: @ShehuGabam, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Shehu Gabam ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Inside Sources'.

Kara karanta wannan

2027: Masari ya taso masu son kawar da Tinubu a gaba, ya fadi makomarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufofin Tinubu za su ba shi matsala

Shehu Gabam ya lissafo wasu daga cikin manufofin Tinubu da ba su yi wa jama’a daɗi ba, da suka haɗa da cire tallafin man fetur, ƙarin kudin wutar lantarki, ƙarin kuɗin sadarwa da sauransu.

"Tinubu yana buƙatar ya sake duba wasu daga cikin manufofinsa, ya sake fasalta majalisar ministocinsa idan yana so ya bar abin da za a riƙa tunawa da shi a cikin shekara biyu."
"Kuma ban ga yadda zai iya tsayawa takara har ya yi nasara a zaɓe ba, da irin waɗannan manufofin da yake aiwatarwa."

- Shehu Gabam

Shugaban na SDP ya ce sukar da ake yi kan gwamnatin Tinubu ta yi kama da wacce aka yi wa tsohon shugaba Goodluck Jonathan a shekarar 2012.

"Zanga-zanga kan Jonathan ta fara bayan shekara biyu a kan mulki, kuma bai tsira ba. Kuma babu wani shugaban ƙasa a tarihin Najeriya da ya kashe kuɗi don sake lashe zabe kamar Shugaba Jonathan."

Kara karanta wannan

"Baki ke yanka wuya," Atiku Abubakar ya jawo wa kansa abin magana kan 'batun N50m'

"Don haka, idan wasu na tunanin amfani da kuɗi zai ba su nasara, suna tafka kuskure. Za ka iya murɗe zaɓe ne kawai idan kana da farin jini."

- Shehu Gabam

Shugaban SDP ya caccaki gwamnatin Tinubu

Shugaban na SDP ya soki gwamnatin Tinubu kan yadda take tsangwamar ƴa adawa, yana mai cewa idan ba ta son a riƙa sukarta, sai ta gyara kundin tsarin mulki domin Najeriya ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya kawai.

“Ba wanda zai iya yi wa gwamna magana, idan ka yi, zai ci maka mutunci, kamar sarki ne da ba a iya tanka masa. Haka wannan gwamnatin take. Da zarar ka ba su shawara, sai su ɗauke ka a matsayin maƙiyi."
"Sun manta cewa wasu jam’iyyun siyasa sun tsaya tsayin daka tare da INEC a lokacin sanar da sakamakon zaɓe, domin ba ma son a shiga ruɗani da hargitsi."

- Shehu Gabam

An caccaki mai goyon bayan Tinubu

Kara karanta wannan

"Za a tsige shi daga shugabancin APC?" An bayyana dalilin naɗa Ganduje a hukumar FAAN

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashi ya tsokano abin rigima, bayan ya bayyana shirinsa na sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu a shekarar 2027.

Mutane da dama sun yi masa rubdugu da baƙaƙen maganganu sakamakon goyon bayan da ya nuna ga Shugaba Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng