Babban Dalilin da Ya Sa Sanatan PDP Ya Jefar da Lema, Ya Sauya Sheƙa zuwa APC
- Hadimin gwamnan jihar Delta ya yi zargin cewa Sanata Ned Nwoko ya bar PDP zuwa APC ne saboda yana tsoron ba zai samu tikiti ba a 2027
- A makon da ya shige ne, sanatan mai wakiltar Delta ta Arewa ya sanar da ficewa daga PDP a wata takarda da ya miƙawa shugabanni a gundumarsa
- Sai dai Fred Oghenesivbe ya ce babu wani rikici da ya kori Nwoko daga jam'iyyar PDP face tsoron ba zai kai labari ba a zaɓe mai zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta - Wani hadimi na Gwamna Sheriff Oborevwori, Fred Oghenesivbe, ya faɗi mahangarsa kan sauya sheƙar sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, Ned Nwoko daga PDP zuwa APC.
Hadimin mai girma gwamnan ya yi zargin cewa sanata Nwoko ya bar PDP saboda yana tsoron ba zai samu tikitin takara ba a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Kamar yadda Punch ta ruwaito, Ned Nwoko ya fice daga PDP a hukumance ranar Juma'a bayan ya miƙa takardar murabus daga zama mamba a gudumarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Nwoko ya fice daga PDP
A cikin wasikar da ya rubuta mai dauke da kwanan wata 30 ga Janairu 2025, Nwoko, ya sanar da gundumarsa da ke karamar hukumar Aniocha ta Arewa cewa ya fice daga PDP.
"Na rubuta wannan wasika ne don sanar da ficewa ta daga PDP, jam’iyyar da na kasance cikinta tun lokacin da aka kafata a 1998.
“Dalilin da ya sa na yanke wannan shawara shi ne rarrabuwar kawuna da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar. Wannan rikici ya sa na ji da wahala mu iya kawo ci gaban al'umma.
"Duk da cewa na yi ban kwana da PDP, ina tabbatar wa ƴan jam’iyyar da magoya bayana cewa a shirye nake na ba da gudummuwa wajen hadin kai da ci gaban Delta ta Arewa.”
- Nde Nwoko.
'Tsoro' ne dalilin ficewar sanatan daga PDP
Sai dai a martanin da ya mayar kan lamarin a ranar Lahadi a Asaba, Oghenesivbe, wanda shi ne Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai da Sadarwa ta Jihar Delta, ya ce:
“Sanata Ned Nwoko ya fice daga jam’iyyar ne saboda yana tsoron cewa ba zai samu tikitin PDP a 2027 ba. Dukkanmu mun san cewa zai fice daga jam’iyyar tun da dadewa.
"Wannan lamari na da alaka da siyasar 2027 da neman tikitin tsayawa takara. Yanzu haka a Delta, Sanata Nwoko ba shi da wata alaka da tsarin PDP, kuma ba ya aiki tare da shugabannin jam’iyyarmu.
"Gwamna Sheriff Oborevwori ne jagoran PDP a jihar Delta, amma Sanata Nwoko ya raba gari da shi. Wanna ya sa yake tsoron cewa ba zai samu tikitin PDP a 2027 ba saboda yadda ya wakilci mutane a matakin kasa.”
Gwamnan Delta na shirin komawa APC?
A wani labarin, kun ji cewa PDP ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa gwamna Sherrif Oborevwori na jihar Delta na shirye-shiryen sauya sheƙa zuwa APC.
PDP ta ce labarin kanzon kurege ne sannan ta bayyana waɗanda suka kirkiro jita-jitar da masu ɗaukar nauyinsu a matsayin waɗanda ba su ƙaunar zaman lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng