Zaben Ciyamomi: APC Ta Kada Jam'iyyun Adawa, Ta Lashe Kananan Hukumomi 16 cikin 18
- APC ta lashe kujerun ciyamomi 16 a zaben kananan hukumomin Ondo, yayin da ake jiran isowar sakamakon zaben garuruwa biyu
- Idan ba a manta ba, PDP ta janye daga shiga zaben, tana mai zargin ODIEC da rashin kwarewa wajen gudanar da sahihin zabe
- An ce, APC ta lashe zaben ne duk da hukumar ODIEC ta soke zaben Ondo ta Yamma saboda amfani da tsohon tambarin jam'iyyar NNPP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi 16 daga cikin 18 da aka gudanar a zaben Ondo.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ondo (ODIEC), Joseph Aremo, ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Akure ranar Lahadi.

Asali: Twitter
Joseph Aremo ya ce an sake jadawalin zaben karamar hukumar Ondo ta Yamma, yayin da ake jiran sakamakon karamar hukumar Owo, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ondo: APC ta lashe zaben kananan hukumomi
Jam’iyyu 12 ne suka tsaya takarar kujerun ciyamomi na kananan hukumomi da kansiloli a zaben da aka gudanar ranar Asabar.
Kafin zaben, jam’iyyar PDP ta janye daga takara, tana mai cewa ba ta yarda cewa ODIEC za ta gudanar da sahihin zabe ba.
Sunayen jam’iyyun da suka shiga takarar sun hada da: Action Alliance, ADP, APP, APC, APGA, Boot Party, da Labour Party.
Sauran sun hada da: National Rescue Party, NNPP, SDP, YPP, da Zenith Labour Party.
Yadda mulkin kananan hukumomi ya gudana
Kafin wannan zaben na Asabar, an gudanar da zabukan kananan hukumomi na karshe jihar a ranar 23 ga Agusta, 2020.
Wa’adin shugabannin kananan hukumomin ya kare ranar 22 ga Agusta, 2023, inda ma’aikatan gwamnati suka karbi ragamar mulki.
Tun daga wancan lokaci, jagororin kananan hukumomi (HODs) ne suke gudanar da ayyukan mulki a kananan hukumomin jihar.
Bayan jan lokaci sau da dama, ODIEC ta tsara ranar 18 ga Janairu, 2025, domin gudanar da zaben kananan hukumomi.
An soke zabe saboda jam'iyyar NNPP
A wani cigaba, ODIEC ta soke zaben da aka gudanar a karamar hukumar Ondo ta Yamma, inji rahoton The Cable.
Hukumar ta ce dalilin soke zaben ya biyo bayan amfani da tsohuwar alamar jam’iyyar NNPP a takardun kada kuri’a.
Shugaban ODIEC, Joseph Aremo, ya ce an sake jadawalin zaben zuwa ranar 19 ga Janairu, 2025.
Ya bayyana cewa an amince da sabon tambarin jam’iyyar ne a karshen shekarar da ta gabata, kuma jam’iyyar ba ta sanar da matsalar da wuri ba.
ODIEC za ta yi zaben Ondo ko ba PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ondo (ODIEC) ta ce za ta gudanar da zaben kananan hukumomi ko ba jam'iyyar PDP.
ODIEC ta jaddada cewa ficewar jam'iyyar PDP daga zaben ciyamomin ba zai kawo mata cikas a shirin da ta yi na yin zaben a ranar 18 ga Janairun 2025 da ta tsara ba.
Asali: Legit.ng