Jam’iyyar NNPP Ta Jawo an Soke Zaben Karamar Hukuma, an Sauya Ranar Zabe

Jam’iyyar NNPP Ta Jawo an Soke Zaben Karamar Hukuma, an Sauya Ranar Zabe

  • Hukumar Zaben Jihar Ondo (ODIEC) ta soke zabe a karamar hukumar Ondo ta Yamma kan tsohon tambarin jam'iyyar NNPP da aka yi amfani da shi
  • Shugaban ODIEC, Joseph Aremo, ya sanar da sake gudanar da zaben a yau Lahadi 19 ga watan Janairu tare da tabbatar da amfani da sabon tambarin
  • Aremo ya bukaci mazauna yankin su kasance masu bin doka da tsari, tare da tabbatar da cewa sauran sakamakon kananan hukumomi ba za su tabu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abeokuta, Ondo - Hukumar Zaben Jihar Ondo (ODIEC) ta soke zaben da aka shirya a karamar hukumar Ondo ta Yamma.

Hukumar ta dauki matakin ne saboda amfani da tsohon tambarin jam’iyyar NNPP madadin sabon da aka sauya.

An soke zabe kan kuskuren jam'iyyar NNPP
Amfani da tsohon tambarin NNPP ya jawo an soke zaben karamar hukuma a Ondo. Hoto: Legit.
Asali: Original

PDP ta fasa shiga zaben karamar hukuma

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Shugaban ODIEC, Joseph Aremo, ya bayyana cewa an amince da sabon tambarin jam’iyyar ne a karshen shekarar da ta gabata, amma ba a lura da matsalar ba, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ayyana Juma’a, 17 ga Janairu, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna Ondo damar yin zaben ciyamomi.

Rundunar 'yan sanda ta hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa a ranar Asabar daga karfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Sai dai jam'iyyar PDP ta sanar da janyewarta daga zaben kananan hukumomin saboda rashin amincewa da tsarin hukumar zabe.

Musabbabin soke zaben karamar hukuma a Ondo

A cewarsa, Aremo ya ce za a gudanar da sabon zaben a yau Lahadi 19 ga watan Janairu, tare da tabbatar da cewa ana amfani da sabon tambarin jam’iyyar NNPP.

Aremo ya bayyana cewa jam’iyyar ta NNPP ta bayyana matsayinta a hukumance, amma shirye-shiryen gudanar da zabe sun riga sun kankama kafin a gyara tambarin, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

Ya tabbatar wa al’umma cewa duk wani shirye-shirye za a kammala kafin zaben da aka sake jadawalin, yayin da sauran sakamakon ba za su sami matsala ba.

Hukumar zaben ta ba yan yankin shawara

Haka kuma, Aremo ya bukaci al’ummar Ondo ta Yamma da su ci gaba da zaman lafiya da kuma shiga cikin sabon tsarin zaben da za a gudanar.

Ya ce babu irin wannan matsalar da aka samu a sauran kananan hukumomi, inda ya tabbatar da cewa matsalar na da alaka da Ondo ta Yamma ne kadai.

“Wannan shawarar ita ce mafi dacewa domin tabbatar da cewa kowace jam’iyya ta samu halin damawa da ita a zaben."

- Joseph Aremo

Gwamna ya sallami dukkan kwamishinoninsa

Kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa gwamnan Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya amince da rusa majalisar zartarwar jihar da yake mulki.

An bar kwamishinan shari’a, Kayode Ajulo da kwamishinar kudi, Omowunmi Isaac, saboda mahimmancin ayyukansu a gwamnati.

Matakin na zuwa ne bayan gwamnan ya samu nasarar lashe zabe karo na biyu, wanda ake gani a matsayin shiri na kafa sabuwar tafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.