Kwankwasiyya Ta Sake Yin Rashi: Fitaccen Mawaki a Arewa Ya Fice daga NNPP zuwa APC

Kwankwasiyya Ta Sake Yin Rashi: Fitaccen Mawaki a Arewa Ya Fice daga NNPP zuwa APC

  • Fitaccen mawaki dan asalin jihar Kano, Ali Isah Jita ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC ta hannun Sanata Barau Jibrin
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau wanda ya tubewa Ali Jita jar hula ya ce yana farin ciki da mawakin ya koma jam'iyyar mai ci
  • A cewar Sanata Barau, Ali Jita ya daukarwa APC alkawarin cewa a shirye yake ya yi aiki tukuru domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fitaccen mawakin soyayya, zamantakewa da ma siyasa, Ali Isah Jita ya hakura da tafiyar Kwankwasiyyya inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sauya shekar Ali Jita na zuwa ne yayin da 'yan Kannywood da dama ke korafin yadda shugabannin Kwankwasiyya ke yi masu rikon sakainar kashi a Kano.

Kara karanta wannan

NNPP ta samu koma baya a Kano: 'Yan TikTok din Kwankwasiyya sun sauya sheka

Sanata Barau I Jibrin ya yiwa Ali Jita maraba da shiga jam'iyyar APC
Abuja: Ali Jita ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC, ya ajiye tafiyar Kwankwasiyya. Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya ce yana yiwa Ali Jita maraba da shiga APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Jita ya koma jam'iyyar APC

Sanata Barau ya nuna jin dadinsa kan yadda fitaccen mawakin da ya ce ya ba da gagarumar gudunmawa a masana'antar nishadi ya koma jam'iyyarsu ta APC.

"Ina yi maka maraba da shigowa jam'iyyar APC, Ali Jita.
"Ali Jita, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa a hFarkar nishadantarwa, ya koma babbar jam’iyyarmu a hukumance bayan ficewar sa daga jam’iyyar NNPP.
"A matsayinsa na matashi mai hazaka, kwarewarsa za ta bunkasa jam’iyyarmu da kuma ba da gudunmawa wajen ci gaban masana’antar Kannywood da harkar nishadi baki daya."

- A cewar Sanata Barau Jibrin

Ali Jita ya yiwa APC alkawari

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya sake yiwa tafiyar Kwankwasiyya illa, jiga jigan NNPP sun koma APC

Mataimakin shugaban majalisar dattawan, ya ce fitaccen mawakin dan asalin jihar Kano ya daukarwa jam'iyyar APC alkawari na tallata dukkanin manufofinta.

A cewar sanarwar Sanata Barau:

"Ali Jita ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki tukuru domin ganin APC ta samu nasara, ya bar tafiyar Kwankwasiyya tare da sadaukar da basirarsa wajen tallafawa manufofinmu.
Muna da yakinin cewa sadaukarwar tasa za ta zaburar da mutane da yawa, kuma ni da kaina ina fatan yin aiki tare da shi yayin da muke ci gaba da karfafa jam’iyyar APC."

'Yan Kannywood sun koma APC

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa shahararrun yan wasan Kannywood, da suka hada da Rabi'u Daushe, Babba Hikima, Hauwa Waraka, Alhaji Habu Tabule da sauransu sun koma APC.

A yayin da ya karbi tawagar jaruman masana'antar ta Kannywood, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa sun yi farin-ciki da dawowarsu APC da ita ce jam'iyya mafi girma a Afrika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.