Sanata Barau Ya Sake Yiwa Tafiyar Kwankwasiyya Illa, Jiga Jigan NNPP Sun Koma APC
- Shugaban ‘yan kasuwar mai da iskar gas na jihar Kano, Hassan Nuhu Hassan, ya fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC a ranar Alhamis
- Hakazalika, shugaban kungiyar ’yan fim ta Arewa, Salisu Muhammed Officer, ya fita daga tafiyar Kwankwasiyya, shi ma ya koma APC
- Wannan na zuwa ne awanni bayan da fitaccen mawaki Ali Jita ya ajiye jar hula ya rungumi tafiyar APC ta hannun Sanata Barau Jibrin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tafiyar Kwankwasiyya ta sake gamuwa da babbar matsala yayin da shugaban masu sayar da man fetur da gas a Kano, Alhaji Hassan Nuhu Hassan ya fice daga NNPP.
Shugaban ‘yan kasuwar mai da iskar gas na Kano, Alhaji Hassan Nuhu Hassan, ya fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC "mafi girma a Afirka," inji Sanata Barau I. Jibrin.
Jigon Kwankwasiyya ya koma APC
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da sauya shekarar Alhaji Hassan a shafinsa na X a daren ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Har ila yau, na karbi bakuncin shugaban ’yan kasuwar mai da iskar gas na jihar Kano, Alhaji Hassan Nuhu Hassan, wanda ya fice daga NNPP zuwa babbar jam’iyyar APC a Afirka."
Sanata Barau ya ce ficewar ‘ya ’yan jam'iyyar NNPP zuwa APC wata shaida ce da ke nuna cewa jama'a sun yaba da ayyukan da suke yi.
Jagoran 'yan Kannywood ya bar NNPP
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa ya karbi bakuncin daya daga cikin shugabannin 'yan wasan Hausa da ya bar tafiyar Kwankwasiyya zuwa APC.
Sanata Barau ya ce:
"Hakazalika, na karbi fitaccen jigo a kungiyar Kwankwasiyya ta Kannywood, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ’yan fim ta Arewa, Salisu Muhammed Officer, wanda ya fice daga NNPP zuwa jam’iyyarmu ta APC.
"Ficewar ‘ya’yan jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyarmu ta APC wata shaida ce da ke nuna cewa al’ummarmu sun yaba da ayyukan da muke yi a jihar Kano baki daya."
Ali Jita ya fice daga NNPP
A ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba ne muka ruwaito cewa Sanata Barau I Jibrin ya karbi Ali Isah Jita wanda ya ajiye jar hula tare da ficewa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Fitaccen mawakin ya sha alwashin yin aiki tukuru domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a siyasarta, lamarin da ya yi wa mataimakin shugaban majalisar dattawa dadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng