"Kanku Ake Ji": El Rufai Ya Bugi Kirji, Ya Yi Zazzafan Martani Kan Zargin Badaƙala a Kaduna

"Kanku Ake Ji": El Rufai Ya Bugi Kirji, Ya Yi Zazzafan Martani Kan Zargin Badaƙala a Kaduna

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya magantu kan binciken da kwamitin Majalisar jihar ta gudanar game da gwamnatinsa
  • El-Rufai ya ce wannan mataki na kwamitin Majalisar kawai bita da kullin siyasa ne amma ya gudanar da gwamnatinsa cikin gaskiya
  • Hakan na zuwa ne bayan kwamitin ya bukaci hukumar yaki da cin hanci ta cafke El-Rufai kan zargin badakala a lokacin mulkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi martani kan zargin badakala a gwamnatinsa.

El-Rufai ya yi fatali da rahoton Majalisar dokokin jihar kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.

El-Rufai ya magantu kan binciken gwamnatinsa da ake yi a Kaduna
Nasiru El-Rufai ya caccaki binciken gwamnatinsa a Kaduna, ya ce bita da kullin siyasa ne. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Twitter

Kaduna: El-Rufai ya magantu kan zargin gwamnatinsa

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Muyiwa Adekeye a yau Laraba 5 ga watan Yuni, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan matakin Majalisar kawai bita da kullin siyasa ne inda ya tabbatar da cewa ya jagoranci gwamnati mai tsafta yayin mulkinsa, Punch ta tattaro.

"Nasir El-Rufai yana alfahari da ayyukan alheri da ya gudanar a jihar Kaduna yayin da ya ke gwamna."
"Mafi yawan wadanda suka yi gwamnati da El-Rufai sun gurfana a gaban kwamitin wanda ke nuna kwarin guiwa kan irin gwamnatin da ya gudanar."
"El-Rufai yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa ya gudanar da mulki cikin gaskiya da bin doka tare da taimakon mukarrabansa kwararru."
"Ya bukaci a yi fatali da wannan bincike na son rai da kuma bita da kullin siyasa da ake yi."

- Muyiwa Adekeye

Majalisar Kaduna ta bukaci gurfanar da El-Rufai

Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar ya bukaci a hukunta El-Rufai da mukarrabansa saboda zargin badakala a gwamnatinsa.

Har ila yau, kwamitin ya bukaci dakatar da kwamishinan kudi a Kaduna, Shizer Badda wanda ya rike mukami a gwamnatin Nasir El-Rufai.

Bello El-Rufai ya magantu kan Uba Sani

Kun ji cewa 'dan Majalisar Tarayya a jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya yi martani kan alakarsa da mai girma Gwamna Uba Sani.

Hon. Bello El-Rufai ya ce har yanzu Mai girma Gwamna Uba Sani mai gidansa ne kuma ya dauke shi abin koyi a rayuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.