Kaduna: Bello El Rufai Ya Yi Ƙarin Haske Kan Alaƙarsa da Gwamna Uba Sani a Yanzu

Kaduna: Bello El Rufai Ya Yi Ƙarin Haske Kan Alaƙarsa da Gwamna Uba Sani a Yanzu

  • Dan Majalisar Tarayya da ke wakilta Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya magantu kan alakarsa a yanzu da Gwamna Uba Sani
  • Bello El-Rufai ya ce har yanzu Uba Sani ne mai gidansa kuma suna gaisawa duk bayan lokaci inda ya ce shi ya daura shi a layi
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin alaka ta kara tsami tsakanin gwamnan da mahaifinsa, Nasir El-Rufai kan bashin Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Dan Majalisar Tarayya a jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya yi martani kan alakarsa da Gwamna Uba Sani.

Bello El-Rufai ya ce har yanzu Mai girma Gwamna Uba Sani mai gidansa ne kuma ya dauke shi abin koyi a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya baro Aiki, ya ce duk wanda ya taba fetur zai yi wuya ya dade a mulki

Bello El-Rufai ya magantu kan alakarsa da Uba Sani
Bello El-Rufai ya bayyana yadda ya ke ganin kimar Uba Sani har yanzu a matsayin mai gidansa. Hoto: @ubasanius, @B_ELRUFAI.
Asali: Twitter

Bello El-Rufai ya yabi Uba Sani

Ɗan tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana haka ne yayin hira da Yaya Abba a wani faifan bidiyon YouTube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce har yanzu suna tare da Sanata Uba Sani kuma babu wata matsala a tsakaninsu kamar yadda da ake tsammani.

Wannan martanin na Bello El-Rufai na zuwa ne yayin da alaka ke kara tsami tsakanin mahaifinsa, Nasir El-Rufai da Uba Sani.

"Aiki da Uba Sani ya koya min darasi na siyasa wanda zai yi amfani matuka a kasar nan."
"Har yanzu mai gida na ne kuma muna magana da shi, lokacin da ya samu tikitin takarar APC ya fadawa mahaifina yana son na nemi takarar dan Majalisar Tarayya."

- Bello El-Rufai

Bello El-Rufai ya fadi kokarin Uba Sani

Ɗan Majalisar ya ce ba mahaifinsa ba ne ya shawarce shi neman takara inda ya ce ko kamfe bai yi masa ba.

Kara karanta wannan

"Daman Kwankwaso bai son Ganduje tun a tashin farko", Farfesa a Kano ya magantu

Ya ce amma Uba Sani ya matsa sai ya koyi wani abu a matsayin hadiminsa lokacin yana Sanata inda ya ce wannan shi ne matakin farko da ya daga shi.

Jigon APC ya magantu kan El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa Jigon jam'iyyar APC, Jesutega Onakpasa ya zargi wasu 'yan siyasa da kawo matsala a cikin jami'yyar da ke mulkin Najeriya.

Barista Onakpasa ya koka kan halin da tsofaffin gwamnoni jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki a yanzu.

Ya bukaci a nemo hanyar gyara matsalar ganin yadda mutanen biyu suka ba da gudunmawa mai karfi wurin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zabe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.