Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban OORBDA, Ya Naɗa Mutum 2 a Manyan Muƙamai

Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban OORBDA, Ya Naɗa Mutum 2 a Manyan Muƙamai

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya shugabancin wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu ranar Laraba
  • Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke da Dokta Adedeji Ashiru a matsayin waɗanda za su jagoranci hukumomin kasar
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya tabbatar da wannan naɗe-naɗen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke a matsayin Darakta-Janar/shugaban hukumar kula da kwararar mai (NOSDRA).

Mista Woke, shi ne shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Ribas a lokacin mulkin tsohon gwamna, Nyesom Wike, ministan Abuja na yanzu.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya naɗa waɗanda za su jagoranci hukumomi 2 na tarayya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Tinubu ya naɗa shugabannin NOSDRA da OORBDA

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada 'dan Arewa a matsayin sabon shugaban hukumar FRSC

Kakakin shugaban ƙasa, Ajure Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, mai girma shugaban ƙasa ya kuma naɗa Dokta Adedeji Ashiru a matsayin shugaban hukumar raya tafkin Ogun-Osun (OORBDA).

Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa sanarwar naɗe-naɗen a shafinsa na manhajar X.

"Shugaban ƙasa na fatan sababbin shugabannin za su baje basira da gogewarsu wajen ɗaga martabar waɗannan hukumomi tare da riko da gaskiya a ayyukan su"

-Ajuri Ngelale.

Shugaba Tinubu ya tsige yaron Wike

Tun da farko, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa shugaba Tinubu ya sauke yaron ministan Abuja, Chukwuemeka Woke, daga kujerar shugaban hukumar OORBDA.

Ya ɗauki wannan matakin ne bayan sukar da ya sha kan naɗin daga manyan ƙusoshin APC da ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Mutane da dama sun fito zanga-zanga kan naɗin Woke a matsayin MD na hukumar, inda suka ce ba ɗan yankin Kudu maso Yamna ba ne.

Kakakin shugaban ƙasa ya ce Tinubu ya maye gurbin Wike da Dakta Adedeji Ashiru.

Bola Tinubu ya naɗa shugaban FRSC

A wani rahoton kuma hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta samu sabon shugaba bayan kammala wa'adin tsohon shugabanta Dauda Ali Biu.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin sabon wanda zai jagoranci hukumar har na tsawon shekara huɗu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel