"Dalilin da Ya Sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi Ba Za Su Kai Labari Ba a Zaɓen 2027"

"Dalilin da Ya Sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi Ba Za Su Kai Labari Ba a Zaɓen 2027"

  • An yi hasashen cewa Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rabiu Kwankwaso ba za su iya kayar da shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2027
  • Fitaccen ɗan fafutukar nan mai haddasa ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, VDM ne ya bayyana haka yayin da ƴan adawa ke shirin haɗa-kai
  • Ya ce shugaban ƙasa Tinubu mutum ne da ya san duk wata hanya da zai samu galaba, saboda haka zai ci gaba da mulki har 2031

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Fitaccen ɗan gwagwarmaya a kafafen sada zumuna, VeryDarkMan (VDM), ya ce ƴan adawa na wasa da ƙaifin basirar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ya jaddada cewa dabarun da Allah ya bai wa Bola Tinubu da ƙarfinsa a siyasa ya zarce wanda ƴan Najeriya suka gani a yanzu.

Kara karanta wannan

"Zamu karɓe wasu jihohi," Ganduje ya bayyana abubuwa 2 da APC ta shirya a 2027

Atiku, Obi da Kwankwaso.
Atiku, Obi da Kwankwaso ba za su iya ja da shugaba Tinubu ba a 2027 Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

VDM ya ba Atiku, Kwankwaso, Obi shawara

Ya kuma gargaɗi ƴan adawa da su yi taka-tsan-tsan kuma su lalubo dabaru na musamman a kokarinsu na ganin sun kifar da wannan gwamnati a zaɓe na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, da wahala ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Mista Peter Obi, ya iya samun nasara a zaɓen 2027, jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya fi karfin hadakar su Atiku

Verydarkman ya yi ƙirarin cewa ƴan takarar jam'iyun PDP da NNPP a 2023, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso, ko ƙanshin kujerar shugaban ƙasa ba za su ji ba.

Ya ce ko da dukkan waɗannan ƴan takara uku sun haɗa kai, abu ne mai matuƙar wahala su iya kifar da shugaban ƙasa mai ci a zaɓen 2027, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi za su haɗa kai da Atiku a 2027, Jigon PDP ya yi bayani

"Na gaji da karanta labarin Atiku da Peter Obi na ƙoƙarin haɗa kai domin karɓe mulki, maganar gaskiya ita ce, Atiku, Obi da Kwankwaso ba za su ji ko da ƙanshin kujerar shugaban ƙasa ba.
"Matsalar ita ce su ƴan adawa suna wasa da kaifin basira da dabarun shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Amma lokaci zai zo, za ku gane babu ɗan siyasa kamar Tinubu.
"Mutumin nan yana da wayo da kaifin hankali. Ya san yadda zai samu abin da yake so. Kada ku yi wasa da shi amma zai ci gaba da zama a ofis har zuwa 2032," in ji shi.

A makon da ya gabata, Peter Obi  ya yi wata ganawar sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a Abuja.

An gano masu kokarin tsige Ganduje

A wani rahoton kuma kun ji cewa Ƙungiyar APC Youth Solidarity Network ta ce yaudararsu aka yi domin su yi zanga-zangar nuna adawa da Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen Atiku ya faɗi lokacin da Peter Obi zai iya hawa mulkin Najeriya

Yan siyasar sun ce maƙiyan jam’iyyar APC ne suka sanya su yi zanga-zangar neman Ganduje ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel