Jerin Gwamnoni 23 da Suka Sauya Sheka Yayin da Suke Mulki Daga 1999 Zuwa Yau

Jerin Gwamnoni 23 da Suka Sauya Sheka Yayin da Suke Mulki Daga 1999 Zuwa Yau

  • Gwamnoni da yawa sun fice daga jam'iyyunsu saboda wasu dalilai na siyasa, a rahoton nan mun tattaro dukkansu
  • Za a ce gwamnonin jihohin Jigawa, Legas da Kebbi sun canza sheka a sakamakon canza sunan jam’iyyun siyasarsu
  • Gwamnoni 7 suka canza shekara daga 2007 zuwa 2015, daga cikinsu akwai ‘yan tawagar G5 da suka fice daga PDP

Abuja - Sauya sheka ba bakon abu ba ne a siyasar duniya, ba a bar Najeriya a baya wajen canza gida a kan mulki ko bayan rasa ofis ba.

Gwamnoni sama da 20 sun bar jam’iyyun da suka lashe zabe zuwa wata jam’iyya dabam.

Gwamnoni
Wasu gwamnonin da suka sauya-sheka a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jihohin da sauyin-shekar gwamnoni ya shahara

Jaridar Leadership ta bibiyi tarihin siyasa tun daga shekarar 1999, ta bibiyi yadda gwamnoni suke ta tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Ganduje: Yadda dakatarwa a mazaba ta kori shugabanni 3 a APC da PDP ana ji ana gani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu jihohin da gwamnoninta suka rika canza gida a shekarun nan kamar Sokoto, Imo da Abia, an samu haka sau bakwai a jihohin uku.

Jam'iyyun da gwamnoni suka sauya-sheka

Jam’iyyun da wannan sauyin sheka ta shafa su ne: APGA, AD, ANPP, PPA, sai APC.

Sauran jam’iyyun siyasar da aka fice daga cikinsu ko aka shigo su a cikin shekarun nan 24 su ne: PDP, AC, LP, ZLP da jam’iyyar DPP.

Legit Hausa tattaro gwamnonin da suka sauya-sheka a lokacin da suke mulki a Najeriya.

Gwamnoni da suka sauya-sheka

1. Attahiru Bafarawa

2. Aliyu Wamakko

3. Aminu Tambuwal

4. Orji Uzor Kalu

5. Theodore Orji

6. Boni Haruna

7. Murtala Nyako

8. Ikedi Ohakim

9. Rochas Okorocha

10. Mahmud Shinkafi

11. Bello Matawalle

12. Abdulfatah Ahmed

13. Isa Yuguda

14. Godwin Obaseki

15. Rabiu Kwankwaso

16. Rotimi Amaechi

17. Saminu Turaki

18. Muhammad Adamu Aleiro

19. David Umahi

20. Ben Ayade

Kara karanta wannan

Tinubu yana amfani da Wike wajen ruguza jam'iyyar PDP? Dele Momodu ya magantu

21. Samuel Ortom

22. Babatunde Fashola

23. Olusegun Mimiko

Attahiru Dalhatu Bafarawa, Aliyu Magatakarda Wamakko da Aminu Waziri Tambuwal duk sun canza shekar siyasa a Sokoto.

Daga jerin za a iya fahimtar cewa a Abia da Imo, sau biyu gwamnoninsu suna canza sheka bayan an zabe su a kan karagar mulki.

Rikici shugaba da 'ya 'yan jam'iyya

Ku na da labarin wasu da suke ikirarin ‘ya ‘yan APC ne suna neman raba Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyya a mazabarsa a Kano.

Ana tsoron idan dakatarwar da aka yi wa shugaban na APC ta zauna, zai iya rasa kujerarsa a NWC kamar yadda aka taba gani a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel