Dalilin barin Saraki da Tambuwal Jam’iyyar APC – Tinubu

Dalilin barin Saraki da Tambuwal Jam’iyyar APC – Tinubu

Mun ji labari cewa babban Jigon APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kaca-kaca da wadanda su ka bar Jam’iyyar APC mai mulki inda yace gigin shugabancin kasar nan ke damun su kuma a-dawo-lafiya.

Dalilin barin Saraki da Tambuwal Jam’iyyar APC – Tinubu
Tinubu yace saraki da Tambuwal na harin kujerar Buhari

Tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu da yake jawabi a Legas yace irin su Bukola Saraki da Aminu Tambuwal sun fice daga APC ne domin sun san ba za su kai labari ba a Jihohin su idan su ka cigaba da zama a Jam’iyyar mai mulki.

Asiwaju Tinubu a jawabin na sa yace wadanda su ka sauya shekar sun bar APC ne domin ba za a ba su tikitin Jam’iyyar a iska ba, kuma dai ba za a bari su rika satar dukiyar Talakawa da wuce gona da iri a kan karagar mulkin su ba.

KU KARANTA: Gwamna Tambuwal yayi wa Marayun Sokoto abin kirki

Bola Tinubu a dogon jawabin da yayi ya kuma sa hannu ya bayyana cewa abin da ya sa Gwamnan Sokoto Waziri Tambuwal ya koma PDP shi ne saboda yana harin kujerar Shugaban kasa kuma ba zai iya yin fito-na-fito da Buhari a APC ba.

Har wa yau babban jagoran na APC yace shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana harin kujerar Shugaban kasar nan don haka ya bar APC. Tinubu yace Saraki na amfani da Majalisar Dattawan ne domin yin abin da ya ga dama

Asiwaju Bola Tinubu ya kara da cewa Gwamnan Ribas Nyesom Wike ne yayi wa Gwamnan na Sokoto alkawarin tikitin Shugaban takarar Shugaban kasa a PDP a 2019 don haka ya bar APC yana labewa da cewa Gwamnatin Shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng