"Ban Son Zama Ubangida" Malam El-Rufa'i Ya Mayar da Martani Kan Abin da Ke Faruwa a Kaduna

"Ban Son Zama Ubangida" Malam El-Rufa'i Ya Mayar da Martani Kan Abin da Ke Faruwa a Kaduna

  • Mallam Nasir El-Rufai ya mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a jihar Ƙaduna karkashin mulkin Uba Sani
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sau biyar kaɗai ya je Kaduna tun bayan sauka mulki saboda ba ya son tsoma baƙi a gwamnati mai ci
  • Wannan kalamai na Mallam Nasiru na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya koka kan tulin bashin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce baya son a kira shi ubangidan siyasa a jihar Kaduna.

Wannan kalamai na Nasir El-Rufai na zuwa ne bayan gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya koka kan tulin bashin da ya gada daga tsohon gwamnan, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa muka gayyaci Nasir El-Rufai zuwa Borno Inji Gwamnatin Zulum

Nasiru Ahmad El-Rufai.
Mallam El-Rufai ya ce ba ya da burin zama ubangida a jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wurin wani taro da aka gayyace shi a jihar Borno ranar Litinin, Mallam El-Rufai ya ce sau 5 kacal ya je Kaduna tun da ya sauka daga mulki, a cewar Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufa'i ya faɗi matsayarsa

A wasu kalamai da ake kallo tamkar martani ne ga rikicin da ke neman kunno kai a siyasar Kaduna, tsohon gwamnan ya ce ba ya tsoma baki a harkokin mulkin Uba Sani.

“Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a al'amuran da ke faruwa a jihar Kaduna, ina son shi (gwamna) ya koya da kansa kuma ya tafiyar da mulki da kansa.
"Abin da muka rasa shi ne shugabanci na gari kuma ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo jagoranci na gari shi ne shugaba ya samu mutanen kirki a kusa da shi domin sauke nauyin da ke kansa.

Kara karanta wannan

Ana kishin kishin din zai sauya sheka, El-Rufai ya ziyarci gwamnan Borno

"Allah SWT ne kaɗai ke da karfin ikon tafiyar da komai da kansa, amma duk yadda shugaba ya kai da zama nagari zai yi tasiri ne daidai gwargwadon mutanen da ke kewaye da shi.

- Malam Nasir El-Rufai

El-Rufai ya ziyarci Gwamna Zulum

A ɗazu mun kawo muku rahoton cewa yayin da ake kishin kishin din zai sauya sheka, Mallam Nasir El-Rufa'i ya sauka a jihar Borno domin gudanar da wani muhimmin al'amari

Wani hadimi ga tsohon gwamnan ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa a ranar Lahadi, 14 ga Afrilu tare da bayyana dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel