Uba Sani Ya Cigaba da Kokawa a Kan Halin da El-Rufai Ya Mika Masa Mulki a Kaduna

Uba Sani Ya Cigaba da Kokawa a Kan Halin da El-Rufai Ya Mika Masa Mulki a Kaduna

  • Mai girma Uba Sani ya yi Allah wadai da irin mummunan halin da ya tsinci manyan asibitoci da ake da su a Kaduna
  • Gwamnan jihar Kaduna ya ce an yi shekaru 20 ba a gyara asibitoci ba, amma ya dauki alkawarin zai gyara matsalolin
  • Sanata Uba Sani ya fadawa masu ruwa da tsaki a APC da gwamnatin Kaduna halin da ya gaji makarantun gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce an shafe shekaru 20 ba tare da gyara manyan asibitocin gwamnati da ke jihar.

A dalilin wannan rashin kulawa da bangaren kiwon lafiya, Uba Sani ya ce mutane suna zuwa neman magani a jihohin makwabta.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya ce asibitoci sun lalace a Kaduna Hoto: @UbaSaniUS
Asali: Twitter

Uba Sani ya hadu da manyan APC

Tribune ta rahoto gwamna yana wannan jawabi lokacin da ya yi zama da masu ruwa da tsaki daga duka kananan hukumomi 23.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya ce asibitocin suna cikin halin ha’ula’i, amma ya kara da cewa a shirye yake ya ga an yi gyare-gyaren da ake bukata.

Gwamna Uba Sani ya koka da asibitoci

Kusan shekara da hawa mulki, ya ce akwai manyan asibitoci shida, biyu daga kowace babbar mazaba da ake da su a Kaduna.

Asibitocin da ake gyarawa a yanzu sun hada da manyan asibitocin da ke Rigasa, Maigana, Gwantu, Kafanchan, Giwa da Ikara.

The Guardian ta rahoto Gwamnan yana cewa bunkasa bangaren kiwon lafiya yana cikin abubuwan da ya sa gaba a jihar Kaduna.

Sani ya ce ya samu rahoto daga mataimakiyar gwamna wanda ta shaida masa duka manyan asibitoci 32 da ke jihar ba su aiki.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

Uba da sauran matsalolin jihar Kaduna

Mai girma gwamnan ya kuma bayyana cewa akwai makarantu fiye da 1, 500 a manyan kananan hukumomi da ba su da katanga.

A jawabin gwamnan, ya ce dole gwamnatinsa ta kawo cigaba a karkara domin manoma kuma sai an samar da tsaro a jihar Kaduna.

Wadanda aka yi zaman da su su ne Dr. Hadiza Balarabe, Air Commodore Emmanuel Jekada (rtd), Hon. Dahiru Liman da manyan APC.

Matsalar wutar lantarki a Najeriya

Kuna da labari cewa a shekarar 1998, ana samar da fiye da megawatt 6, 000 lantarki, amma yanzu karfin wutan ya ja da baya.

Daga 1999 zuwa 2007, an kashe fiye da $13bn domin inganta wuta, amma har yau ana cikin duhu don haka ne ake so a yi bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel