Bello El-Rufai Ya Bayyana Adadin Miliyoyin da Mahaifinsa Ya Ba Shi da Ya Fito Takara

Bello El-Rufai Ya Bayyana Adadin Miliyoyin da Mahaifinsa Ya Ba Shi da Ya Fito Takara

  • Muhammad Bello El-Rufai ne ya yi wa jam’iyyar APC takarar ‘dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a zaben 2023
  • Duk da yana sabon ‘dan siyasa, babban yaron gwamnan ya samu karbuwa musamman ganin yadda yake bada taimako
  • A lokacin mahaifinsa ne gwamna a jihar Kaduna, N5m ya ba shi a matsayin gudumuwarsa wajen yakin neman takara a APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Muhammad Bello El-Rufai ya yi wata doguwar hira a watan nan na Maris, inda ya tattauna a game da batutuwa da yawa.

Seun Okinbaloye ya zanta da Hon. Muhammad Bello El-Rufai a shirinsa Mic On, inda ‘dan majalisar ya bada labarin yakin zabensa.

Bello El-Rufai
Hon. Bello El-Rufai da mahaifisa, Nasir El-Rufai Hoto: @B_ElRufai
Asali: Twitter

Gudumuwar El-Rufai ga 'dansa a zaben 2023

Kara karanta wannan

Kakakin kwamitin kamfen Atiku ya faɗi muhimman abubuwa 2 da Najeriya ke buƙata kafin zaɓen 2027

‘Dan majalisar mai wakitar Kaduna ta Arewa ya ce a lokacin da yake neman takara a 2023, Naira miliyan biyar mahaifinsa ya ba shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da Bello El-Rufai ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilan tarayya, mahaifinsa Nasir El-Rufai shi ne gwamnn Kaduna.

Takarar Bello El-Rufai zuwa majalisar tarayya

A cewar ‘dan majalisar, a lokacin Mai girma Uba Sani yana Sanata, sai ya kawowa gwamnan shawarar takarar Bello El-Rufai a 2023.

Kamar yadda ya shaida a shirin na Podcast, Malam Nasir El-Rufai bai yi maraba da shawarar nan ba saboda wasu dalilai da ya kawo.

El-Rufai ya so takarar yaron da ya haifa?

Daga ciki shi ne tsohon gwamnan na Kaduna bai son ganin ana neman maida mulkin tamkar wani gadon gidan Nasir El-Rufai.

‘Dan majalisar ya kuma ce daga baya mahaifinsa ya bayyana masa yana da saurin fushi, saboda haka bai dace da wakilcin jama'a ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauko mutumin Buhari ya ba shi shugabancin hukumar kula da almajirai

An bijiro batun takarar ne a birnin Dubai, Malam Bello El-Rufai ya so a ce gudumuwar yakin zaben da gwamna ya ba da ya wuce N5m.

Bello El-Rufai ya zama wakili a majalisa

Yayin kamfe, Bello El-Rufai ya shiga kowace mazaba da ke Kaduna ta Arewa, kuma a karshe ya tashi da kuri’u fiye da 51, 000 a APC.

Kamar yadda babban yaron gwamnan ya fada, sun yi tsari da kyau, tun kafin ya lashe zabe yake bada tallafi, a karshe ya doke PDP.

‘Dan siyasar ya jero inda suka sha bam-bam da mahaifin nasa, daga ciki shi ne ko kadan Malam El-Rufai bai sha’awar kujerar majalisa.

An hana El-Rufai zama ministan tarayya

A baya ana da labari dan majalisar tarayya, Bello El-Rufai ya fadi yadda ya ji bayan kin amincewa da mahaifinsa ya zama minista.

Nasir El-Rufai ya samu matsala a majalisa yayin tantance wadanda za su zama ministoci, inda aka fake da wani rahoton tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel