Bello El-Rufai ya taya Mahaifin sa murnar lashe zaben Kaduna

Bello El-Rufai ya taya Mahaifin sa murnar lashe zaben Kaduna

Dazu nan ne aka sanar da sakamakon zaben jihar Kaduna inda aka sanar da cewa gwamna Nasir El-Rufai ya doke ‘dan takarar babbar jam’iyyar hamayya na PDP watau Honarabul Isa Ashiru Kudan.

Bello El-Rufai wanda shi ne babban yaron gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya taya Mahaifin na sa murnar lashe zaben da yayi. Bello yake cewa ‘Dan takarar PDP, Isa Ashiru yayi kokarin gaske a wajen yakin neman zaben.

A shafin Tuwita, Bello El-Rufai ya bayyana cewa babban abokin takarar na gwamna El-Rufai ya jajirce yadda ya kamata, Bello El-Rufai yace Isa Ashiru Kudan bai kama layin da irin su Sanata Shehu Sani na PRP su ka kama ba.

KU KARANTA: ‘Dan takara ya samu kuri’a 100, 000 ba tare da yayi yawon kamfe ba

Bello El-Rufai ya taya Mahaifin sa murnar lashe zaben Kaduna
‘Dan Gwamnan Kaduna ya yabawa dattakun 'Dan takarar PDP
Asali: UGC

Yaron gwamnan ya kuma jinjinawa yadda jama’ar Kaduna su ka tsaya wajen sake marawa Nasir El-Rufai baya a zaben na bana. Haka kuma El-Rufai ya soki Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani wanda yace ya kawowa jihar cikas.

Mista El-Rufai ya kuma yi addu’a Ubangiji ba shugabannin jihar ikon gyara kura-kuran da su kayi a baya. A jawabin da Matashin yayi a Tuwita, ya kuma nemi a zauna cikin hadin-kai da kaunar juna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel