Bai Son Kujerar, Bello El-Rufai Ya Fadi Asarar da Aka Yi Kan Rashin Mahaifinsa a Gwamnatin Tinubu

Bai Son Kujerar, Bello El-Rufai Ya Fadi Asarar da Aka Yi Kan Rashin Mahaifinsa a Gwamnatin Tinubu

  • Bello El-Rufai, dan Majalisar tarayya a Kaduna ya bayyana irin rashin mahaifinsa da ‘yan Najeriya za su yi a cikin gwamnatin Tinubu
  • El-Rufai wanda ‘da ne ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana takaicinsa kan kin amincewa da mahaifin nasa a Majalisa
  • Ya ce tun farko tsohon gwamnan bai son mukamin su ne suka matsa masa domin ya karbi kujerar a gwamnatin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Dan Majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya ce Najeriya ta rasa jigo bayan majalisa ta ki amincewa da mahaifinsa.

El-rufai ya ce kin amincewa da Majalisar ta yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai babbar asara ce ga kasar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon kwamandan Hisbah ya tona asirin wasu 'yan siyasa kan dambarwar da ta faru kan hukumar

Bello El-Rufai ya fadi suka yi ta rokon mahaifinsa kafin amincewa da mukamin Minista
Bello ya ce tun farko El-Rufai bai son mukamin su ne suka matsa masa. Hoto: @B_ELRUFAI.
Asali: Twitter

Yadda Bello suka roki El-Rufai kan mukamin Minista

Bello ya bayyana haka ne yayin hira da dan jarida Seun Okinbaloye da Punch ta ruwaito inda ya ce mahaifin nasa tun farko ba ya son mukamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sai da suka hadu da shi da sauran iyalansu domin rokon tsohon gwamnan ya karbi mukamin minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Ya kara da cewa ya ji takaici sosai bayan kin amincewa da mahaifinsa a Majalisar inda ya ce tabbas an tafka babban rashi a wannan gwamnati.

“Ina cikin Majalisar lokacin da aka ki amincewa da mahaifina, na ji takaici a lokacin kuma har yanzu ina jin zafin haka.”
“Da ni da gwamnan Kaduna, Uba Sani da wani kwamishina a lokacin mulkin mahaifina mun taka rawa sosai wurin rokonsa domin ya karbi mukamin.”
“Tun farko shi ba ya bukatar mukamin, amma zai yi wahala ‘yan Najeriya su yarda da haka saboda sun yi tsammani kowa ya na son mukamin Minista.”

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

- Bello El-Rufai

Bello ya bayyana halin mahaifinsa

Bello ya ce tabbas ba ya son mukamin mune muka matsa masa amma kuwa da ya karba za a samu sauyi a wannan gwamnati matuka, cewar Ripples.

“Shugaba Tinubu ya na son yin aiki tare da shi domin har Kaduna ya zo kan lamarin, mun yi tunanin zai ba shi ma’aikatar makamashi ko kuma iskar gas.”
“Mutane da yawa basu san mahaifina ba, mutum ne mai saukin kai amma ana yi masa mummunan fahimta.”

- Bello El-Rufai

Bello ya soki malamin Musulunci

Kun ji cewa, Bello El-Rufai ya soki malamin Musulunci a Sokoto da ya yi wasu kalamai kan matar shugaban kasa, Remi Tinubu.

Bello ya ce a yanzu ba a bukatar tubar malamin ya kamata a dauki mataki a kansa saboda ya zama izina ga saura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel