Kano: Jami'yyar NNPP Ta Kifar da APC a Zaben Cike Gurbi a Wata Mazaba a Jihar, Bayanai Sun Fito

Kano: Jami'yyar NNPP Ta Kifar da APC a Zaben Cike Gurbi a Wata Mazaba a Jihar, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da aka gudanar da zaben cike gurbi a fadin Najeriya, INEC ta fara sanar da sakamakon zaben da aka gudanar
  • Hukumar ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a mazabar Rimin Gado/Tofa a Majalisar jihar Kano
  • INEC ta ayyana Bello Muhammad na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.

INEC ta fitar da sanarwar ce kan sakamakon zaben cike gurbi a mazabar Rimin Gado/Tofa a Majalisar jihar Kano.

INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben cike gurbi a Kano
Bello Butu-Butu ya lashe zaben cike gurbi a Kano. Hoto: Muhammad Bello.
Asali: Facebook

Waye hukumar INEC ta sanar ya lashe zaben?

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta bayyana jami'yyar da ta yi nasara a zaben maye gurbin Gbajabiamila, an fadi kuri'u

Hukumar ta ayyana Bello Muhammad Butu-Butu na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya ce jam'iyyar NNPP ta samu kuri'u 31,135 a zaben.

Yayin da jam'iyyar APC mai adawa a jihar da dan takararta suka samu kuri'u 25,577 a zaben da aka gudanar a yau Asabar 3 ga watan Faburairu.

An gudanar da zaben cike gurbi a jihohi 26

A yau ne aka gudanar da zaben cike gurbi a fadin kasar baki daya wanda ya kunshi jihohi 26 da ke Najeriya.

Har ila yau, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Legas.

Hukumar ta bayyana Fuad Laguda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Surulere a Majalisar Wakilai.

Kara karanta wannan

Kano: An gano wadanda suka dauki nauyin ta'addanci a zaben cike gurbin jihar, NNPP ta yi martani

INEC ta sanar da Ehindero wanda ya lashe zabe

Kun ji cewa Hukumar zabe ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe a mazabar Akoko da ke jihar Ondo a Majalisar Tarayya.

Hukumar ta ayyana Ifeoluwa Ehindero na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar.

Faresa Johnson Fasinmirin shi ya ayyana Ehindero a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel