Kano: An Gano Wadanda Suka Dauki Nauyin Ta’addanci a Zaben Cike Gurbin Jihar, NNPP Ta Yi Martani

Kano: An Gano Wadanda Suka Dauki Nauyin Ta’addanci a Zaben Cike Gurbin Jihar, NNPP Ta Yi Martani

  • Yayin da aka samu tashe-tashen hankula a zaben cike gurbi, jam’iyyar NNPP rashen jihar Kano ta yi martani
  • Jam’iyyar ta bayyana rashin jin dadinta ganin yadda APC ta dauki hayar ‘yan daba don kawo cikas a zaben
  • Shugaban jam’iyyar, Hashim Suleiman Dungurawa shi ya bayyana haka a yau Asabar 3 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP a Kano ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan masu zabe a jihar.

Jam’iyyar ta bayyana rashin jin dadinta ne ta bakin shugabanta a jihar, Hashim Suleiman Dungurawa, cewar Vanguard.

NNPP ta yi martani kan rikicin jihar a zaben cike gurbi da ake yi
An Gano Wadanda Suka Dauki Nayin Ta’addanci a Zaben Cike Gurbin a Kano. Abba Kabir.
Asali: Twitter

Martanin jami'yyar NNPP kan rikicin

Lamarin kamar yadda ta bayyana ya faru ne a yau Asabar 3 ga watan Faburairu yayin gudanar da zaben cike gurbi a jihar.

Kara karanta wannan

CAN ta tilasta dan takara janyewa dan jam'iyyar PDP a zaben cike gurbin Taraba? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a mantaba a yau ne aka gudanar da zaben a mazabar Kunchi/Tsanyawa da ke Majalisar jihar.

Dungurawa ya ce:

“Mun samu bayanan kai hare-hare kan masu zabe don kawo cikas da kuma hana yin zabe a mazabun.
“Tun a daren jiya Juma’a muka gano dubban ‘yan daba da jam’iyyar APC ta dauki hayarsu don kawo cikas a zaben.”

An soke zaben cike gurbi a Kano

Jam’iyyar ta kuma godewa jami’an tsaro da kokarin kare rayukan jama’a a wuraren da aka gudanar da zabukan, cewar BusinessDay.

Har ila yau, bayan samun tashe-tashen hankula a yankin, Hukumar INEC ta soke zaben da aka gudanar.

Hakan ya biyo bayan samun rikici da ya hada da satar akwatunan zabe da kuma ayyukan ta’addanci a wurin.

Daga bisani, jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cewa sun kama matasa da dama da zargin kawo cikas a zaben.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

INEC ta soke zaben Kano

Kun ji cewa Hukumar zabe a INEC ta soke zabukan da aka gudanar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom.

Hukumar ta dauki matakin ne bayan samun tashe-tashen hankula a mazabun da ake gudanar da zaben.

A jihar Kano, hukumar ta soke zaben ne a mazabar Kunchi/Tsanyawa da ke karamar hukumar Kunchi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel