Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Takaddamar Zaben Gwamnan PDP, Ta Fadi Dalili

Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Takaddamar Zaben Gwamnan PDP, Ta Fadi Dalili

  • Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara
  • Kotun ta sake tabbatar da nasarar Gwamna Fubara na jam'iyyar PDP a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar
  • Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Tonye Cole saboda rashin gamsassun hujjoji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Rivers.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Siminalayi Fubara na PDP a matsayin halattaccen gwamnan jihar, cewar Channels TV.

Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan PDP
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fubara a Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara, Tonye Cole.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar jihar Rivers?

Kara karanta wannan

PDP vs APC: Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar gwamnan jihar Sokoto

Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Tonye Cole saboda rashin gamsassun hujjoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ta ke tabbatar da nasarar Fubara, kotun ta ce masu daukaka kara ba su kawo gamsassun hujjoji da ke tabbatar da korafinsu ba.

Dan takarar APC na kalubalantar zaben Fubara inda ya ce gwamnan bai yi murabus ba a matsayin Akanta Janar a jihar Rivers.

Korafe-korafen dan takarar APC a Rivers

Har ila yau, ya na kalubalantar zaben inda ya ce akwai kura-kurai da kuma saba dokar zaben da hukumar INEC ta fayyace, cewar TheCable.

Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto a yau Alhamis 25 ga watan Janairu.

Har ila yau, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmad Aliyu na APC a matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukuncin karshe kan zaben gwamnan APC, komai na iya faruwa

Wannan na zuwa ne bayan kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sa'idu Umar saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kotun Koli ta shirya raba gardama kan zaben Rivers

Kun ji cewa Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Rivers.

Kotun ta tanadi hukunci ne kan takaddamar da ake yi tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Tonye Cole.

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Fubara na jam'iyyar PDP a matsayin halattaccen zababben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel